Da alama sojojin Sudan sun mayar da martani ga kungiyar RSF a karshen shekarar da ta gabata, inda suka mamaye tsakiyar Sudan kafin su ƙwato kusan babban birnin kasar baki daya.

Sojojin Sudan sun yi ikirarin ƙwace filin jirgin saman Khartoum daga hannun RSF

Sojojin Sudan sun sake ƙwace iko da filin jiragen sama na Khartoum daga hannun dakarun Rapid Support Forces, in ji wata majiyar soji, yayin da sojojin suka yi ƙawanya ga wuri mafi girma na karshe da ke hannun 'yan tawayen a kudancin birnin.

Sojojin da ke fafatawa da RSF tun daga watan Afrilun 2023, sun “ƙwace gaba daya” filin jirgin saman da ke tsakiyar birnin Khartoum daga mayakan RSF da ke ciki, in ji majiyar a ranar Laraba, inda suka bukaci a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin bayani ga manema labarai.

Bayan ƙwato Fadar Shugaban Ƙasar da aka yi a wata muhimmiyar nasara a ranar Juma'a, sojojin kasar sun kutsa cikin tsakiyar birnin Khartoum, inda suka ƙwace cibiyoyin gwamnati da RSF suka kama a farkon yakin, kafin su nufi kudu.

Majiyar ta ce "A kudancin babban birnin kasar, sojojin mu sun kewaye yankin Jebel Awliya mai muhimmanci daga bangarori uku: arewa, kudu da gabas," in ji majiyar, inda ta ƙara da cewa "ana kutsawa dukkan sauran yankunan sannu a hankali".

Gadar Jebel Awliya, wacce ta ratsa Kogin White Nile a kudancin tsakiyar birnin, ita ce hanya daya tilo daga yankin da har yanzu ke karkashin ikon kungiyar RSF, wanda ke danganta kungiyar da ke da alaka da tungarta a yammacin yankin Darfur.

A ko ina cikin birnin, shaidun gani da ido da masu fafutuka sun bayar da rahoto a wannan makon cewa mayakan na RSF suna ja da baya a kudu daga unguwannin da suke iko da su a baya, watau Jebel Awliya.

RSF ba ta mayar da martani ba nan take da aka nemi jin ta bakinta.

An kwashe mutane daga yankin RSF

Tun daga watan Afrilun 2023, yakin ya kashe dubba mutane, ya raba fiye da mutum miliyan 12 da muhallansu tare da haifar da rikicin yunwa da ƙaurace mafi girma a duniya.

Yaƙin ya ɗaiɗaita Khartoum ta yadda ta sauya gaba ɗaya.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutume miliyan 3.5 ne aka tilasta wa tserewa daga babban birnin kasar, lamarin da ya bar yankunan ba kowa.

Wasu miliyoyi, ba za su iya ko ba sa son barin ƙasarsu, an bar su suna fuskantar yunwa, cin zarafi da kuma luguden wuta a kan gidajensu daga bangarorin biyu.

Majiyoyin lafiya biyu sun ce RSF din ta ƙwace asibitin Tamayoz da ke kudancin filin jirgin, wanda tun farkon yakin suka yi amfani da shi wajen kula da mayakan nasu.

Osama Abdel Qader, wani mazaunin unguwar Sahafa da ke kusa, ya bayyana a ranar Laraba cewa, "Yankin ya kasance babu kowa daga cikin dakarun rundunar RSF tun daren jiya."

A yankin South Belt babban birnin kasar, inda masu fafutuka suka ba da rahoton wasu munanan take hakkin yaƙin, Issa Hussein ya ce: "Rundunar RSF ba ta da ƙarfi a kan tituna tun ranar Lahadi".

“A jiya na ga motoci bakwai (RSF) dauke da kayan gidai da iyalai sun nufi Jebel Awliya,” in ji shi.

Tun lokacin da aka fara yakin, ana zargin kungiyar ta RSF da wawashewa da kuma ƙwace gidajen mutane, inda kungiyoyin kare hakkin bil adama ke tattara bayanan cin zarafin mata da sauran cin zarafi.

Bayan da aka shafe watanni ana shan kaye, a karshen shekarar da ta gabata ne sojojin kasar suka yi yunkurin juyin mulki, inda suka ratsa tsakiyar kasar Sudan kafin su kwato kusan babban birnin kasar baki daya.

#