Rundunar sojin ta ce Abu Asad, wanda babba ne a kungiyar Ali Ngulde da ke karkashin Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda kamar Ibrahim Nakeeb da Mujaheed Dimtu da Mustafa Munzir da sauran mayaka na daga cikin wadanda jirgin saman ya yi wa luguden wuta
Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta ce ta halaka gomman ‘yan ta’adda a wani hari da ta kai tsaunin Mandara, inda ta ce ta kawar da wasu daga cikin manyan 'yan kungiyar
Sojojin sama na Operation Hadin Kai ne suka kai wannan harin a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwambar 2023, inda sojojin suka ce wannan samamen nasu na daga cikin mafi nasara a tarihin rundunar ta Operation Hadin Kai.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin sama Edward Gabkwet ya fitar, sojojin sun kai wa ‘yan ta’addan hari a yayin da ‘yan ta’addan suka taru a kusa da wasu gidaje uku masu rufin kwano wadanda bishiyoyi suka zagaye su.
“Daga bidiyon da aka dauka, da alama ‘yan ta’addan sun taru ne a wurin domin gudanar da wata tattauna da suka shirya ko kuma shirya wani babban hari.
“Sama da 'yan ta'adda 100 dauke da muggan makamai ne aka gansu suna ta mu’amula da juna tare da shawagi a kusa da gine-ginen wadanda a kusa da su akwai motoci hudu na daukar soji,” in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta ce bayan samamen da dakarunta suka kai sun gano cewa dakarun nata sun lalata gine-gine biyu cikin uku da ke wurin sannan an lalata motocin ‘yan ta’addan baki daya.
“Haka kuma akwai alamun Abu Asad, wanda babba ne a kungiyar Ali Ngulde da ke karkashin Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda kamar Ibrahim Nakeeb da Mujaheed Dimtu da Mustafa Munzir da sauran mayaka duk suna daga cikin ‘ya ta’addan da aka kashe a harin.”
Arewa Maso Gabashin Nijeriya na daga cikin yankunan kasar da ke fama da rikicin ‘yan ta’addan Boko Haram, duk da cewa jami’an tsaron kasar na cewa suna samun nasara kan ‘yan ta’addan.
Domin ko a cikin wannan watan na Nuwamba sai Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun kasar sun kashe ’yan kungiyar Boko Haram/ISWAP da sauran 'yan bindiga 113 kuma sun kama mutum 300 bayan wasu jerin farmaki da suka kai bangarori dama na kasar a cikin mako daya.