Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce akwai bukatar a san cewa ba ita kadai ke amfani da jiragen yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba.
Rundunar sojin saman Nijeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa jirgin yakinta ya kai hari kan masu bikin Maulidi a Kaduna.
Tun da safiyar Litinin ne wasu daga cikin kafafen watsa labaran Nijeriya suka rinka ruwaito cewa jirgin sama wanda ake zargin na sojojin saman Nijeriya ne ya kai hari a Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare a ranar Lahadi.
“Labaran da ke yawo wanda ake zargin Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta kai hari bisa kuskure kan farar hula a Kaduna ba gaskiya bane,” kamar yadda mai magana da yawun sojin saman Nijeriya Edward Gabkwet ya sanar.
“Akwai bukatar a san cewa sojojin sama ba su kai wani samame a Kaduna a sa’o’i 24 da suka gabata ba. Haka kuma akwai bukatar a san cewa ba Rundunar Sojin Saman Nijeriya ce kadai ke amfani da jirage marasa matuka na yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba,” in ji sanarwar.