Ya ce dakarun kasar na rundunar Operation Hadin Kai sun kama kayayyakin Boko Haram da na Kungiyar ISWAP a Kukawa da Damboa da Monguno da Karamar Hukumar Konduga a jihar Borno da ke a yankin arewa maso gabashin kasar.
Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun kasar sun kashe ’yan kunigyar Boko Haram/ISWAP 113 kuma sun kama 300 bayan wasu jerin farmaki da suka kai bangarori dama na kasar a cikin mako daya.
Daraktan Yada Labaran HedIkwatar Tsaron Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai kan aikace-aikacen rundunar sojin kasar a Abuja ranar Alhamis.
Har ila yau ya ce dakarun sun kama masu satar man fetur su 25 kuma sun kubutar da mutum 91 da aka sace. Kazalika ya ce sun gano makamai guda 129 da albarusai 717.
Ya ce dakarun kasar na rundunar Operation Hadin Kai sun kama kayayyakin Boko Haram da na Kungiyar ISWAP a Kananan Hukumomin Kukawa da Damboa da Monguno da Konduga a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Mai magana da yawun rundunar ya ce sun kashe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP 17, sun kama 16 kuma sun ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su da kuma kama albarusai iri daban-daban yayin farmakin da suka kai.
Ya ci gaba da cewa rundunar Operation Hadin Kai a ranar 2 ga watan Nuwamba, ta kawar da masu tayar da kayar baya da dama da kuma lalata kayayyakinsu a yankin Degbewa.
Manjo Janar Buba ya ce a shiyyar tsakiyar kasar rundunar Safe Haven ta gudanar da wasu ayyuka a wani bangare na jihohin Kaduna da Filato, inda ta kashe ’yan bindiga biyar ta kama 14 kuma ta kubutar da mutum 15 da aka yi garkuwa da su.
A cewarsa Rundunar Whirl Stroke ta gudanar da wani farmaki a wani wuri da ake zargin maboyar miyagun mutane ne a wasu bangarorin jihohin Nasarawa da Benue da kuma Filato, inda aka kawar da ’yan bindiga biyu, aka kama 10 kuma aka kubutar da mutum uku da aka yi garkuwa da su.
A arewa maso yamma, dakarun rundunar Hadarin Daji sun kawar da ’yan bindiga 30, da kama wasu bakwai tare da kubutar da mutum 31 da aka yi garkuwa da su a Katsina da Kebbi da kuma Zamfara yayin farmakin, a cewarsa.
Ya ce dakarun kasar sun gano bindigogi kirar AK47 guda 15 da bindiga samfurin RPG Tube da bam guda biyar da gurneti shida da kakin soji biyar da sauransu.
Haka dai mai magana da yawun hedkwatar tsaron kasar ya yi zayyana nasarorin da dakarun sojin kasar suka samu yayin ganawa da manema labaran.