Wata sanawa da muƙaddashin jami’in watsa labaran rundunar, Kyafin Mohammed Goni, ya sanya wa hannu ranar Litinin ta ce rundunar ta yi nasarar kashe ‘yanta’addan ne tsakanin ranar 10 zuwa ranar 18 ga watan Oktoba na shekarar 2026.
Rundunar Operation Haɗin Kai mai yaƙi da ta’addanci a arewa maso gabashin Nijeriya ta ce hare-haren da dakarunta suka kai ta sama sun yi sanadin kashe ‘yanta’adda 103 a cikin kwanaki takwas.
Wata sanawa da muƙaddashin jami’in watsa labaran rundunar, Keftin Mohammed Goni, ya sanya wa hannu ranar Litinin kuma aka wallafa a shafin Facebook na sojin Nijeriya ta ce rundunar ta yi nasarar kashe ‘yanta’addan ne tsakanin ranar 10 zuwa ranar 18 ga watan Oktoba na shekarar 2026.
Sanarwar ta ce dakarun sun cim ma nasarar ce ta hanyar haɗa ɓangaren sama na sojin Nijeriya da kuma jirage mara matuƙa na sojin, lamarin da ya sake tabbatar da jajircewar sojin wajen kassara ‘yanta’addan da kuma hana su yin aika-aika.
“Hare-haren sama babu ƙaƙƙautawa sun haɗa da samame bakwai kan wuraren da ‘yanta’adda suke a ƙaramar hukumar Guzamala ranar 10 ga Oktoba da Badu a ƙaramar hukumar Monguno ranar 11 ga watan Oktoba da Mairari a ƙaramar hukumar Guzamala da wani ɓangare da ke gar da Badu ranar 13 ga Oktoba,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ce wuraren sun haɗa da Duste Uku a ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa ranar 16 ga watan Oktoba, da kuma ɗaya daga cikin gidaje biyu na Abu Saleem, Walin ISWAP na kudancin Tafkin Chadi, a yankin Arina Woje da ke ƙaramar hukumar Monguno ta jihar Borno ranar 18 ga Oktoba.
Kyaftin Goni ya bayyana cewa a harin da rundunar ta kai a gidan Abu Saleem ta yi nasarar kashe Jindullah, babban jami’in tsaron Abu Saleem da kuma Abul Kissa, wani mamba a kwamitin shura na ƙungiyar ta’addancin.
“Harin ya lalata ginin da kuma muhimman kayayyakin sufuri, ciki har da injunan kwale-kwale tara da wasu babura da aka adana a cikin gidan,” in ji sanarwar, tana mai ƙarawa da cewa harin ya lalata tsarin ƙungiyar na ɓoye abubuwa a daji.
“Daga farko, a ranar 13 ga watan Oktoba kayan aikin sama mai suna Guardian ya bi ‘yanta’adda 16 daga yankin Mairari zuwa wani taron fiye da ‘yanta’adda 100 tare da babura, misalin kilomita 23 gabar da Badu kuma kilomita 19 yamma da ƙaramar hukumar Monguno,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa harin da aka kai kan taron ya kashe kimanin ‘yanta’adda 30, yayin da ba tabbatar da abin da ya faru da baburan ba.
Kazalika sanarwar ta ce cikin lokacin rundunar ta kai hare-hare kan ‘yanta’adda da kayayyakinsu a Gudumbali da Badu, Mairari da kuma Duste Uku, tana mai cewa hare-hare bakwai ɗin sun yi silar mutuwar ‘yanta’adda 103 da kuma lalata cibiyoyin zirga-zirga da kuma adana kayayyakinsu.

