Shugaban rundunar sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa Janar Abdourahamane Tiani ne ya jagoranci kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.

Sojojin Nijar sun 'amince da sharuddan mika mulki' ga gwamnatin farar-hula

Sojojin Nijar sun amince da sharuddan mika mulki ga gwamnatin farar-hula, kuma za su gabatar da tsarinsu na yin haka ga kungiyar ECOWAS, a cewar wani jam'in diflomasiyyar kasar Togo wadda ke shiga tsakanin bangarorin biyu.

Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey ne ya bayyana haka ranar Alhamis a wata hira da gidan talbijin na Jamhuriyar Nijar.

Ya ce an cim ma yarjejeniya "game da lokaci da kuma tsare-tsaren" mika mulki a ganawarsu da Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine da ministan harkokin waje Bakary Yaou Sangare.

"Mun shirya gabatar da tsare-tsare... ga shugabannin kasashen da ke shiga tsakani da kuma Majalisar ECOWAS," in ji shi.

ECOWAS ta sanya wa sojojin Nijar jerin takunkumai ciki har da na rufe kan iyakokin mambobinta da katse lantarki da ake ba ta daga Nijeriya da kuma dakatar da kasar daga harkokin kudi na kungiyar, tun da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Takunkumai masu tsauri

Takunkuman da aka sanya wa Nijar da kuma cire ta daga cikin harkokin kasashen duniya sun jefa ta cikin karin matsin tattalin arziki.

A watan Oktoba, shugabannin sojojin sun sanar da rage kashi 40 cikin dari na kasafin kudin kasar na 2023 "sakamakon takunkuman da kasashen duniya da na lardi suka sanya mana".

A taron ECOWAS na ranar Lahadin da ta gabata, shugabanninta sun gindaya wa sojojin Nijar sharudda kafin su cire musu takunkumai.

#