Tasirin Faransa ya yi matuƙar raguwa a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka na Yammacin Afirka irin su Mali, Burkina Faso da Nijar, bayan sun raba gari da ita inda suka ƙulla ƙwance da Rasha.
Sojojin Faransa da aka kora daga wasu ƙasashen Afirka sakamakon juyin mulkin soji za su zauna a Chadi domin ci gaba da gudanar da ayyukansu, a cewar wani wakili na musamman na shugaban Faransa Emmanuel Macron ranar Alhamis.
Tasirin Faransa ya yi matuƙar raguwa a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka na Yammacin Afirka irin su Mali, Burkina Faso da Nijar, bayan sun raba gari da ita inda suka ƙulla ƙwance da Rasha.
Yanzu haka Faransa ta jibge dakaru kusan 1,000 a Chadi, ƙasar da Janar Mahamat Idriss Deby Itno yake jagoranta tun daga 2021 bayan mutuwar mahaifinsa.
"Tabbas za mu zauna a Chadi", in ji Jean-Marie Bockel, wakilin Macron na musamman a Afirka wanda aka ɗora wa alhakin gudanar da sabuwar tattaunawa kan makomar Faransa a nahiyar.
Macron ya buƙaci tattaunawa da hukumomin Chadi game da yadda Faransa za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukan soja a nahiar Afirka a ganawar da ya yi da Deby Itno a N'Djamena, a cewar Bockel.
Kazalika Bockel ya ce ya shaida wa Deby Itno buƙatar Faransa wajen ganin Chadi ta koma turbar dimokuraɗiyyya bayan ta kwashe fiye da shekara talatin tana ƙarƙashin mulkin soja wanda mahaifinsa ya shugabanta.
Deby Itno zai yi takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar ranar 6 ga watan Mayu kuma ana ganin shi ne zai yi nasara a zaɓen saboda ya kori manyan ƴan adawa daga ƙasar, yayin da aka ɗaure wasu sannan aka kashe wasu.
A makon jiya ne aka kashe babban mai hamayya da shi Yaya Dillo Djerou, wanda kuma danginsa ne a wata fafatawa da ya yi da sojojin ƙasar. Gwamnati ta ce Dillo ya ƙi amincewa ya miƙa kansa ga sojoji.