Sport
Dollar
38,8949
0.36 %Euro
43,4533
-0.25 %Gram Gold
3.997,1000
-0.9 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%An tafi da Succes Masra, wanda ke jagorantar 'yan adawa a Chadi zuwa wani wuri da ba a san ko ina ba ne, in ji jam'iyyarsa.
An tafi da tsohon Firaministan Chadi kuma shugaban jam'iyyar adawa daga gidansa a ranar Juma'a, a cewar jam'iyyarsa.
"An yi amfani da karfin soja wajen tafiya da Succes Masra daga gidanmu a ranar Juma'a, 16 ga watan Mayu, da misalin karfe 5:56 na safe," a cewar sakon da jam'iyyar ta wallafa a Facebook.
Wani sakon da Ndolembai Sade Njesada, mataimakin shugaban jam'iyyar adawa ta Transformers karkashin jagorancin Masra ya wallafa a shafin Facebook, ya nuna hotunan wasu mutane sanye da kayan soji da kuma makamai suna tafiya da Masra daga gidansa da ke zama hedkwatar jam'iyyar.
Kawo yanzu dai gwamnati ba ta ce uffan ba kan lamarin.
Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby ya nada Succes Masra a matsayin firaminista a watan Janairun 2024.
Masra ya yi takara da Deby a zaben shugaban kasa a watan Mayun 2024 kuma ya yi murabus bayan sakamakon zaben da aka yi ta ce-ce-ku-ce a kai, inda aka zabi Deby a matsayin shugaban kasa.
Mahamat Idriss Deby ya hau karagar mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar mahaifinsa shugaba Idriss Deby Itno, a fagen daga.
Takarar zabe
Mutuwar shugaban a lokacin ta janyo samar da gwamnatin rikon kwarya ta soji, yanayin da ya bai wa dansa damar karbar ragamar jagorancin Majalisar Rikon kwarya ta Soja a kasar.
A cikin watanni, Mahamat Deby ya yi alkawarin cewa za a gudanar da zabe bayan mika mulki a watanni 18 na mulki rikon kwarya na soji inda za a mika mulkin ga farar hula.
Sai dai a watan Oktoban 2022, kungiyar Tattaunawa ta Kasa ta kara wa'adin mika mulki da wasu shekaru biyu, wanda ya ba shi damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2024, kana ya lashe zaben da kashi 61% na kuri'un da aka kada.
Succes Masra ya fafata da Deby duk da kasancewarsa firaiminista a lokacin, ya samu kashi 18.5% na kuri'un da aka kada kuma ya kalubalanci sakamakon zaben.
Comments
No comments Yet
Comment