A shekarar da ta gabata ne wata kotun ƙasar Finland ta ɗaure Simon Ekpa, wani jigo a cikin ƙungiyoyin da ke neman kafa ƙasar Biafra, a kudu maso gabashin Nijeriya.
Wata kotun ƙasar Finland ta rage ɗaurin da aka yi wa shugaban ‘yan a-waren Nijeriya da ke neman kafa ƙasar Biafra, Simon Ekpa da aka samu da laifin ‘ta’addanci’ daga shekara shida zuwa huɗu.
A shekarar da ta gabtaba, kotun Paijat-Home ta samu Simon Ekpa, mai shekara 41 da ke da shaidar ɗan ƙasar Nijeriya da Finland, da laifi bisa taka rawa a harkokin wata ƙungiyar “ta’addanci” da kuma tunzura mutane aikata laifuka don dalilai na “ta’addanci.”
Kotun ta gano cewa wani babban jigo ne a cikin ƙungiyoyin da ke neman kafa ƙasar Biafra, a kudu maso gabashin Nijeriya, inda wani yaƙin basasa da aka yi tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 ya kashe ɗaruruwan dubban mutane.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin ƙaramar kotu, inda ta same shi da laifi bisa laifuka na “ta’addanci”, da aka aikata a wani ɓangare na kafafen sada zumunta yayin da yake zama a birnin Finland na Lahti tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024.
Amma kotun ta rage ɗaurin da aka masa da shekaru biyu domin "yanayin" da ya kewaye matakan da aka ɗauka kan batun kafa ƙasar Biafra.