Shugaban Laberiya George Weah ya kira abokin hamayyarsa Joseph Boakai ta wayar tarho inda ya amsa shan kaye sannan ya taya shi murna.

Shugaban Liberia George Weah ya amsa shan kaye a zaben shugaban kasar

Shugaban Laberiya George Weah ya amsa shan kaye a hannun jagoran 'yan hamayya kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai a zaben da aka gudanar a farkon makon nan.

Boakai ya samu kashi 50.89 na kashi 99.58 na akwatunan zaben da aka kidaya, a cewar sakamakon zaben da shugabar hukumar zabe Davidetta Browne Lansanah ta sanar ranar Juma'a. Weah ya samu kashi 49.11.

“Sakamakon zaben da aka sanar da daddare, duk da yake ba shi ne na karshe ba, ya nuna cewa Ambasada Joseph Boakai ne a kan gaba kuma ba za a iya kamo shi ba. Don haka, mintunan da suka gabata, na yi magana da zababben shugaban kasa Joseph Boakaiinda na taya shi murna,” in ji Weah.

“A yayin da muke magana a kan sakamakon zaben, ya kamata mu sani cewa mutanen da suka yi nasara ta hakika su ne al'ummar kasar Laberiya,” a cewarsa.

Weah ya bayyana cewa gogayyar da aka yi a lokacin zaben ta fito da babbar barakar da ke tsakanin 'yan kasar.

#