Publication : 16 February 2026
Update : 16 February 2026
Murabus ɗin ya zo ne a tsakiyar ce-ce-ku-ce da rikici cikin hukumar
Rahotanni daga Nijeriya na cewa shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya ajiye aikinsa a daidai lokacin da ake shirye-shiryen aikin Hajjin 2026.
TRT Hausa
Har zuwa yanzu ba a bayyana dalilin murabus ɗin ba, sai dai kafofin watsa labaran Nijeriya sun ambato Ahmed Muazu, mai magana da yawun shugaban, yana tabbatar da cewa Sheikh Pakistan ya ajiye mukaminsa.
TRT Hausa
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Sheikh Pakistan a matsayin shugaban NAHCON a shekarar 2024 bayan cire Jalal Arabi, wanda a wancan lokaci aka fara bincike a kansa bisa zargin yin ba daidai ba da kuɗaɗen aikin hajji.
TRT Hausa
A shekarar 2025, Sheikh Pakistan ya jagoranci aikin hajji na farko a matsayinsa na shugaban hukumar, sai dai daga baya shugabancinsa ya fuskanci ce-ce-ku-ce da zarge-zargen badaƙalar kuɗi a aikin hajjin shekarar.
TRT Hausa
Zarge-zargen sun haifar da rikici a cikin hukumar tare da jawo hankalin jama’a, inda aka yi ta musayar yawu kan yadda aka tafiyar da kuɗaɗe da harkokin aikin hajjin.
TRT Hausa
A watan Janairun 2026, rahotanni sun ce wasu kwamishinonin NAHCON sun rubuta takardar ƙorafi zuwa ga Shugaba Tinubu, suna zargin shugaban hukumar da gazawa wajen shugabanci da rashin kyakkyawan tsarin gudanarwa.
TRT Hausa
Rikicin ya tilasta mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima shiga tsakani, inda ya kira taron masu ruwa da tsaki kimanin makonni biyu da suka gabata domin sasanta rikicin da dawo da zaman lafiya a cikin hukumar.
TRT Hausa
Uganda's ex-military intelligence officer extradited to US to face arms smuggling charges
A former confidant of Uganda's army chief has been extradited to the United States for allegedly plotting to provide weapons to Mexican drug cartels.
Six Nigerian imams abducted on their way to pray for president's re-election
Armed men, locally known as bandits, have kidnapped six imams in a northern Nigeria, police said on Sunday.
Most Read
All rights reserved. Newstimetr © 2023