An naɗa Farfesa Mustapha Aliu domin wakiltar yankin Arewa maso Yamma, wanda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru, yayin da Bashir Muhammed Umar zai wakilci yankin Arewa ta Tsakiya, don maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu.

Shugaba Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe a Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC)

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya zaɓi mutum huɗu a matsayin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), da wasu mutum biyu a matsayin Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (RECs), domin cike guraben da ake da su sakamakon ƙarewar wa’adin wasu jami’an hukumar.

Waɗannan naɗe-naɗe, waɗanda ke buƙatar tantancewa da amincewar Majalisar Dattawa, sun haɗa da sake naɗa Dr. Bala Bila a matsayin Kwamishinan Ƙasa mai wakiltar yankin Arewa maso Gabas.

An naɗa Farfesa Mustapha Aliu domin wakiltar yankin Arewa maso Yamma, inda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru, yayin da Bashir Muhammed Umar zai wakilci yankin Arewa ta Tsakiya, inda zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu.

Tinubu ya kuma zaɓi Oluwatoyin Babalola, wadda a halin yanzu ita ce Kwamishiniyar Zaɓe ta Jihar Osun, a matsayin kwamishiniyar ƙasa mai wakiltar yankin Kudu maso Yamma. Ana sa ran za ta maye gurbin Farfesa Cornelius Ajayi, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 24 ga Oktoba.

Mutum biyun da aka zaɓa domin mukaman Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (RECs) su ne Dr. Samuel Akinjide Akinleye, tsohon babban sakatare mai ritaya, wanda aka zaɓa domin wakiltar Jihar Ekiti, da kuma Zahradden Basiru Sanusi daga Jihar Jigawa, wanda zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.

Shugaban ƙasar ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta gaggauta kammala aikin tantancewa da tabbatar da naɗe-naɗen, gabanin babban zaɓen da ake shirin gudanarwa a watan Janairu.

Waɗannan naɗe-naɗe sun zo ne a daidai lokacin da INEC ke shirye-shiryen babban zaɓen ƙasar, inda ake sa ran naɗawa da tabbatar da kwamishinonin zai taimaka wajen cike guraben da ke cikin shugabancin hukumar.

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance waɗanda aka zaɓa kafin yanke hukuncin amincewa ko ƙin amincewa da naɗe-naɗensu.

 

 

#