Allah Ya yi wa fitacciyar tauraruwar finafinan Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da Saratu Daso rasuwa.
Allah Ya yi wa fitacciyar tauraruwar finafinan Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da Saratu Daso rasuwa.
Ta rasu ne ranar Talata a birnin Kano da ke arewacin Nijeriya.
Shugaban hukumar tace finafinai na jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha ya ce Daso ta rasu ne "bayan kwanciya barci da ta yi bayan gama sahoor."
Danginta sun ce za a yi jana'izarta bayan la'asar.
Daso tana cikin taurarin finafinan Kannywood da aka daɗe ana damawa da su.
Baya ga harkar fim, marigayiyar tana gudanar da gidauniya ta musamman wadda ke taimaka wa marayu da marasa galihu.