Kudirin 'ya nuna rashin jituwar da ke tsakanin kwamitin sulhu da ƙasashen duniya,' in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Turkiyya.

Sake nazarin bai wa Falasdinu damar zama mamba a MDD 'muhimmin ci gaba ne' —Turkiyya

Turkiyya ta yaba da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya bai wa Falasdinu damar samun ƙarin hakki tare da sake yin la'akari da barin ta ta zama mamba, inda ta kira hakan "babban ci gaba."

Wakilin Turkiyya a Majalisar Dinkin Duniya Ahmet Yildiz ya shaida wa babban zauren Majalisar Dinkin Duniyaranar Litinin cewa, "amincewa da wannan ƙudiri ba wai kawai wani gagarumin ci gaba ne a yunƙurin Falasdinu na neman zama ƙasa ba, har ma yana ƙara nuna rashin jituwar da ke tsakanin Kwamitin Sulhu Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashen duniya.

Da yake bayyana cewa amincewa da kudurin a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana matsayin hadin gwiwar Ƙasashen Duniya, Yildiz ya ce, Turkiyya na alfahari da daukar nauyin wannan ƙuduri mai cike da tarihi."

Da yake jaddada mummunan halin da ake ciki a Zirin Gaza da Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, Yildiz ya ce, "an yi wa al'ummar Falastinu mummunar illa, tare da yin watsi da dokokin ƙasa da ƙasa."

Har ila yau ya nuna matuƙar damuwarsa kan sabon halin da ake ciki a Rafah da ma sauran yankunan kasar, yana mai jaddada cewa, gano manyan kaburbura a Zirin Gaza na nuna irin tsananin halin da ake ciki.

"Yunwar da mutane suka haddasa"

"Al'ummar Gaza na fuskantar bala'i na yunwa. UNRWA, kashin bayan ayyukan jinƙai a Gaza, na fuskantar hare-hare ta siyasa da ta zahiri. Ruguza muhimmin aikin UNRWA ba wai kawai ta'azzara wahala zai yi ba, har ma ya dagula al'amuran yankin baki daya," in ji shi.

Da yake lura da tsananin damuwar da ake ciki game da rikicin jinƙai da ake ci gaba da fama da shi a Gaza, Yildiz ya ce: Rashin iya dakatar da zubar da jini da yunwa da mutane ke fama da su a Gaza abin takaici ne kuma abin kunya ne."

Ya kuma jaddada bukatar Ƙasashen Duniya na tsagaita bude cikin gaggawa, da shigar da agajin jinƙai ba tare da tsangwama ba, da kuma kawo karshen gudun hijira da ake tilasta wa mutanen yankin suna yi.

Da yake jaddada rashin mutunta matakin da kotun kasa da kasa ta dauka na wucin gadi, da shawarwarin kwamitin sulhu kan taimakon jinƙai, da kuma muhimman ka'idojin dokokin kasa da kasa," Yildiz ya ce: "Mafi girman keta dokokin MDD yana faruwa a gaban idanunmu a Gaza, tare da yunkurin cin mutuncin Majalisar Dinkin Duniya da Yarjejeniyarta a karkashin wannan zauren. "

Ƙwararan matakai na cimma samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu

Ya kuma jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya tsakanin kasashe biyu don hana sake afkuwar tashe-tashen hankula, inda ya bayar da shawarar shigar da Falasdinu a matsayin cikakkiyar mamba a MDD.

"Turkiyya tana goyon bayan shigar da Falasdinu a matsayin cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya," in ji Yildiz, yana mai jaddada cewa irin wannan matakin zai bai wa Falasdinawa damar cimma burinsu na samun kasa da kuma 'yancin kai.

Yildiz ya bukaci Kwamitin Sulhun da ya dauki kwararan matakai wajen ganin an samar da mafita ta siyasa bisa hangen nesa na kasashe biyu da kuma iyakokin da suka gabata kafin shekarar 1967, tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birnin kasar Falasdinu mai cin gashin kanta."

#