Daraktan Sadarwar Fahrettin Altun ya ce taimakon jinƙai da matsayar siyasa da Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta a kan lamarin Isra'ila da Falasdinu a baya-bayan nan sun tabbatar da ƙoƙrin Turkiyya da iyawarta a kan al'amuran duniya.

Sabon karnin Jamhuriya zai zama shi ne Karnin Turkiyya: Altun

Ana girmama Turkiyya a ƙasashen duniya kuma tana samun nasara a muhimmiyar rawar da take takawa, musamman a kan al'amuran da suka shafi yankin, ciki har da lamarin Gabas ta Tsakiya da kafatanin yankin Asiya, in ji daraktan sadarwa na ƙasar.

A wata maƙala da aka wallafa a Jaridar Daily Express ta Birtaniya da Interfax ta Rasha, Daraktan Sadarwar Fahrettin Altun ya ce taimakon jinƙai da matsayar siyasa da Shugaba Tayyip Erdogan ke jagoranta a kan lamarin Isra'ila da Falasdinu a baya-bayan nan sun tabbatar da ƙoƙrin Turkiyya da iyawarta a kan al'amuran duniya.

"Kamar yadda aka gani a kan sha'anin Ukraine da Karabakh da sauran al'amuran da suka shafi yankin, a yayin da muke shiga ƙarni na biyu na zamowar Turkiyya Jamhuriyar, ƙasar ta zamo wata mai faɗa a ji a yankin," in ji Altun.

#