Kamfanin dillancin labarai na KAN ya ce rundunar sojin Isra'ila na shirin yin amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta don sake shirya dakarunta a shirye-shiryen fadada hare-hare ta kasa a kudancin Gaza.

Rundunar Sojin Isra'ila ta amince da yarjejeniyar sakin fursunonin yaki, da tsagaita wuta na wucin gadi da Hamas

Kamfanin dillancin labarai na KAN ya ce rundunar sojin Isra'ila na shirin yin amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta don sake shirya dakarunta a shirye-shiryen fadada hare-hare ta kasa a kudancin Gaza.

Rundunar sojin Isra'ila ta amince da yarjejeniyar musayar wadanda aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta na wucin gadi da kungiyar Falasdinawa ta Hamas a Zirin Gaza, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Talata.

"Rundunar soji na shirin yin amfani da tsagaita wuta domin sake shirya dakarunta a shirye-shiryen fadada kai hare-haren ta kasa zuwa kudancin Gaza," a cewar kafar yada labarai ta KAN.

A cewar kafar yada labaran, yarjejeniyar da aka cimma ta hada da tsagaita wuta na kwanaki hudu, da kuma sakin wasu ‘yan Isra’ila 50 da Hamas ke garkuwa a musayar Falasdinawa 150 da ke gidajen yarin Isra’ila.

Isra'ila ta yi kiyasin cewa akalla Isra'ilawa 239 ne Hamas ke tsare da su bayan harin da aka kai kan iyaka a ranar 7 ga watan Oktoba.

Isra'ila ta kai hare-hare ta sama da ta kasa a Zirin Gaza bayan harin ba-zata na Hamas, inda ta kashe Falasdinawa sama da 14,128, ciki har da yara 5,840 da mata 3,920, a cewar hukumomin lafiya a yankin.

Dubban gine-gine, da suka hada da asibitoci da masallatai da majami'u aka rusa ko lalata a hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama da ta kasa kan yankin da aka yi wa awanya.

Adadin wadanda suka mutu a Isra'ila, ya kai kusan 1,200, a cewar alkaluman hukuma.

#