Publication : 5 February 2026
Update : 5 February 2026
Matakin ya biyo bayan ƙarin haɗin gwiwa kan yaƙi da ta’addanci a Yammacin Afirka
Amurka ta tura wata ƙaramar tawagar jami’an sojinta Nijeriya, kamar yadda babban jami’in rundunar sojin Amurka a Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson, ya bayyana ranar Talata. TRT Hausa
Janar Anderson ya ce matakin ya biyo bayan wata ganawa da Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da aka yi a birnin Roma a shekarar da ta gabata, inda ɓangarorin biyu suka amince da buƙatar ƙara matsa ƙaimi wajen yaƙi da barazanar ta’addanci a Yammacin Afirka. TRT Hausa
Ya bayyana cewa tura sojojin ya ƙunshi ƙaramar tawagar Amurka da ke zuwa da ƙwarewa ta musamman domin taimaka wa ƙoƙarin da Nijeriya ke yi na shawo kan matsalolin tsaro. TRT Hausa
A watan Disamban 2025, Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da izinin kai wasu hare-hare a Nijeriya, tare da nuna yiwuwar ƙara ɗaukar matakan soji a ƙasar. TRT Hausa
Washington ta ƙara sanya ido kan Nijeriya bayan Trump ya zargi ƙasar da gaza kare al’ummar Kiristoci, inda ya yi barazanar ɗaukar matakan soji a matsayin martani. TRT Hausa
Sakamakon haka, an ayyana Nijeriya a matsayin ƙasa da ake nuna damuwa a kanta dangane da ‘yancin addini, wata sifa da majalisar dokokin Amurka ke amfani da ita kan ƙasashen da ake zargi da danniya a fannin addini. TRT Hausa
Sai dai gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da zargin kisan kiyashi ga Kiristoci, tana mai cewa ƙungiyoyi masu makamai na kai hare-hare ne kan fararen-hula ba tare da bambancin addini ba. TRT Hausa
Xenophobia: Nigeria bans legislators from working with South Africa
The assembly says the ban extends to "virtual/online engagements".
King Oyo: Uganda government races to resolve succession row before Saturday burial
The kingdom says King Oyo's funeral cannot proceed unless agreement is reached on who succeeds him.
Most Read
All rights reserved. Newstimetr © 2023