Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Isra'ila tana rasa goyon baya saboda yadda take kai hare-haren kan "mai-uwa-da-wabi" a Gaza da aka mamaye inda ya yi kira ga Benjamin Netanyahu ya canza gwamnatinsa, abin da ya fito da rashin jituwar da ke ts

Rikici ya kaure tsakanin Biden da Netanyahu kan hare-haren Gaza

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya kamata Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sauya tsattsauran ra'ayin gwamnatinsa inda ya ce nan gaba ba zai yiwu Isra'ila ta hana tabbatar da kasar Falasdinu ba, sai dai Netanyahu ya yi raddi cewa Amurka ta jefa "bama-bamai masu guba" a Japan.

Biden ya yi tsokacin ne a wurin bikin tara masa kudi na yakin neman zabensa na 2024 bayan Amurka ta sayar wa Isra'ila tankokin yaki 14,000 ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ba sannan ta hau kujerar-na-ki lokacin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya nemi amincewarta game da kudurin da ke neman Isra'ila ta tsagaita wuta a Gaza.

Biden ya shirga karya cewa "galibin kasashen duniya suna goyon bayan" Isra'ila, duk kuwa da zanga-zangar da ake ta gudanarwa a fadin duniya na kyamarta tun daga 7 ga watan Oktoba sannan kasashe mambobin Kwamintin Tsaro na MDD da ma mambobin Babban Zauren MDD sun yi tarayya wajen kira a kawo karshen cin zalin da Isra'ila take yi wa al'ummar Gaza.

"Amma yanzu su (Isra'ila) sun soma rasa goyon baya saboda yadda suke kai hare-haren bama-bamai irin na kan mai-uwa-da-wabi," in ji Biden.

Biden ya yi wadannan kalamai ne a yayin da mai ba shi shawara kan sha'anin tsaro, Jake Sullivan, take shirin tafiya Isra'ila domin tattaunawa da majalisar da ke aiwatar da yaki ta kasar.

Biden ya ambaci dan siyasar Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir, wanda shi ne ministan tsaron kasa na Isra'ila, inda ya ce "wannan ce gwamnati mafi tsattsauran ra'ayi a tarihin Isra'ila."

"Ya kamata [Netanyahu] ya canza gwamnatinsa. Wannan gwamnatin ta Isra'ila tana sanya abubuwa suna yin tsauri," a cewar Biden. Ya ce nan gaba ba zai yiwu Isra'ila "ta ki yarda" a kafa kasar Faladinu ba, matakin da masu tsattsauran ra'ayi na Isra'ila suke adawa da shi.

#