NiDCOM ta ce tsare su ba tare da bayyana laifi ba na nuna wariya ga ’yan Nijeriya

Nijeriya ta buƙaci Mozambique ta saki ’yan ƙasarta 42 da aka kama

Gwamnatin Nijeriya ta buƙaci mahukuntan ƙasar Mozambique su gaggauta sakin ’yan Nijeriya 42 da aka bayar da rahoton kama su ba tare da bayyana takamaiman laifin da suka aikata ba.

Shugabar Hukumar ’Yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta yi Allah wadai da kamen tare da bayyana shi a matsayin abin damuwa.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, Dabiri-Erewa ta buƙaci mahukuntan Mozambique su saki mutanen ko kuma su gurfanar da su a gaban kotu idan akwai laifin da suka aikata.

Ta ce tsare ’yan Nijeriyar ba tare da bayyana laifinsu ba abin takaici ne, musamman ganin cewa rahotanni sun nuna cewa ’yan Nijeriya kaɗai aka kama a wurin.

Rahotanni sun ce an kama mutanen ne yayin wani samame da aka kai a wata kasuwar sayar da kayan gyaran motoci (spare parts), inda aka kama ’yan Nijeriya yayin da aka bar ’yan kasuwar sauran ƙasashe da ke wurin.

A cewar NiDCOM, hakan na nuna yiwuwar wariya ko nuna ƙyama ga ’yan Nijeriya.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an tabbatar da cewa mutanen da aka kama suna zaune a ƙasar bisa ƙa’ida, kuma ofishin Jakadan Nijeriya bai samu rahoton wata tuhuma da aka shigar kansu ba.

Har ila yau, rahotanni sun nuna cewa an doki wasu daga cikinsu lokacin da ake kama su, an kwashe musu kayayyakinsu, sannan wasu da dama sun kamu da rashin lafiya a gidan yari kuma suna buƙatar kulawar likitoci.

Dabiri-Erewa ta buƙaci gwamnatin Mozambique ta tabbatar da tsaro da lafiyar waɗanda aka tsare yayin da ake ƙoƙarin warware matsalar.

Tushen labari: Newstimehub

 
 
 
 
 
#