NFF ta ba shi alhaƙin kai Super Eagles gasar kofin duniya ta 2026 kuma za a ci gaba da buga wasannin neman shiga gasar ne a watan Maris.

NFF ta naɗa Eric Chelle a matsayin sabon kocin Super Eagles

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta naɗa Éric Sékou Chelle a matsayin babba kocin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya, Super Eagles.

Wata sanawar da hukumar ta fitar a shafukanta na sada zumunta, ta ce hukumar ta yi naɗin ne bisa shawara daga wani kwamitinta.

“A zamansa da aka yi a Abuja ranar Alhamis biyu watan Janairun shekarar 2025, kwamiti na dabaru da ci-gaba ta ba da shawarar naɗa tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafar Mali a matsayin sabon kocin Super Eagles. Kwamitin zartarwa na hukumar NFF ya amince da shawarar ranar 7 ga watan Janairu,” in ji sanarwar.

“Chelle, wanda ya yi wa tawagar Aiglons ta Mali jagoranci a wasanni biyar baya ga kasancewa kocin kulob-kulob kamar su GS Consolat da FC Martigues da Boulogne da kuma MC Oran, ya jagoranci tawagar Aiglons tun shekarar 2022,” a cewar NFF.

Mali ta zo kusa da samun gurbi a matakin dab da na ƙarshe a gasar AFCON ta shekarar 2023 da aka yi inda Cote d’Ivoire ta doke Mali da 2-1.

Cote d’Ivoire ce dai ta lashe kofin AFCON na gasar 2023 bayan ta doke Nijeriya a wasan ƙarshe na gasar da aka yi a filina wasan Alassane Ouattara a Abidjan.

“Kocin mai shekara 47 da haihuwa ya murza leda a Martigues da Valenciennes da Lens da Istres da kuma Chamois Niortais a Faransa a lokacin da yake ɗan wasa,” in ji sanarwar.

NFF ta ba shi alhaƙin kai Super Eagles gasar kofin duniya ta 2026 kuma za a ci-gaba da buga wasannin neman shiga gasar ne a watan Maris.

Wannan shi ne kusan karon farko da tawagr Super Eagles za ta sami koci ɗan Afirka da ba Nijeria ba

#