"Ƙasashen Yamma sun gaza kare kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa kuma sun ƙi goyon bayan gaskiya a tarihi a kan Bosnia, Kosovo, Iraƙi da Syria. Wannan karon lamarin ya bambanta. Mutane suna cewa, 'Wannan zaluncin ya isa haka," Erdogan ya
"A halin yanzu ɗan'adam yana cikin halin ha'ula'i. Waɗanda suke bin tafarkin gaskiya na tarihi su ne suke magana," a cewar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da yake magana a kan batun cin zalin da Isra'ila ke yi a Gaza, bayan dawowarsa daga wata ziyarar diflomasiyya da ya kai Aljeriya.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da yake cikin jirgi, Shugaban Kasar ya yi Allah wadai da mamayar da Isra'ila ke yi, yana mai alaƙanta ta da fashi da makami, tare da jaddada yadda matsayar ƙasashen duniya ke sauyawa ta ƙin goyon bayan Isra'ila.
“Lokaci ya sauya. Kuna iya ganin yadda duniya ta fara daukar mataki kan Isra'ila. Yayin da wasu gwamnatoci suka yi shiru kan mamayar da ake yi a Gaza, Alhamdu lillahi lamarin ya ankarar da mutane gane daidai da rashin adalci. Yawan wadanda ke goyon bayan Falasdinu a kan tituna na karuwa,” in ji shi.
Da yake ba da misali da gangamin da aka yi kwanan nan a Berlin da Birtaniya da Amurka da sauran ƙasashe, ya bayyana yadda ake samun ƙaruwar fafutuka har ma a cikin isra'ilan, inda mutane ke yin kira ga Firaminista Netanyahu ya sauka daga mulki.