"Muna fuskantar hatsari, kuma akwai yiwuwar fuskantar barazana ta gaza dakatar da abin da ke faruwa," in ji Hakan Fidan.

Ministan Wajen Turkiyya ya yi gargaɗi  kan yiwuwar ɓarkewar rikici saboda harin da Amurka ke kai wa ƙungiyoyin da Iran ke goyon baya

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargadi game da yiwuwar watsuwar rikici a Gabas ta Tsakiya a yayin da Amurka ke matsa kaimi wurin kai hare-hare kan kungiyoyin da Iran take goyon baya.

"Idan kana wasa da wuta, mai yiwuwar wutar ta zama tamkar gobara wadda ba za a iya shawo kanta ba. Muna fuskantar hatsari, kuma akwai babbar barazana ta yiwuwar gaza shawo kan abin da zai faru," a cewar Fidan a wata hira da gidan talbijin na kasa ranar Lahadi.

Fidan ya ce Turkiyya tana tattaunawa da Amurka da sauran kasashen da ke yankin a-kai-a-kai , yana mai karawa da cewa: "Akwai bukatar mu guje wa watsuwar rikicin zuwa wasu sassan yankin. Halin da ake ciki ba mai kyau ba ne. Za mu iya fuskantar watsuwar rikicin sosai."

Da yake magana game da masu bijiro da batun tsaron Isra'ila a koyaushe, Fidan ya ce babban abin da Isra'ila ta sanya a gaba shi ne fadada iyakokinta maimakon tsaronta.

Isra'ila za ta samu zaman lafiya ne idan ta daina "shirga karga" ga kasashen duniya sannan ta bari Falasdinawa suka samu kasa mai ƴancin kanta, a cewar ministan harkokin wajen na turkiyya.

Fidan ya jaddada tunatarwa ga kasashen yankin waɗanda suka sha alwashin cewa a shirye suke su ɗauki nauyin tabbatar da zaman lafiya, inda ya ce: "Lokacin da muka bijiro da batun samar da ƙasashe biyu masu ƴancin kansu, babban burinmu shi ne mu kasance masu shiga tsakani wajen tabbatar da hakana."

#