Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan na ci gaba da kokarin diflomasiyya na ganin an warware bala'in da ke shafar bil'adama a Gaza yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan na ci gaba da kokarin diflomasiyya na ganin an warware bala'in da ke shafar bil'adama a Gaza yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a yankin da aka yi wa ƙawanya.
A ranar Litinin din nan ne Fidan ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da takwararsa ta kasar Holland Hanke Bruins Slot da kuma na Czech Jan Lipavsky domin tattauna halin da ake ciki a yankin, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.
Fidan ya shaida wa Slot cewa ya kamata a sanar da tsagaita wuta cikin gaggawa, sannan kuma a kai agajin jinƙai zuwa Gaza cikin gaggawa, in ji majiyoyin.
Ya kuma ce kamata ya yi a yi hadin gwiwa don hana ta’azzarar rikicin a Gaza da hana bazuwa a rikicin yankin.
A yayin tattaunawar ta wayar tarho, manyan jami'an diflomasiyyar sun kuma yi musayar ra'ayi kan halin da ake ciki a Ukraine yayin da ake ci gaba da yaƙin Rasha da maƙwabciyarta.
Majiyar ta ƙara da cewa, Fidan ya jaddada muhimmancin farfaɗo da yarjejeniyar hatsi ta Bahar Aswad.
A hannu guda kuma, Fidan ya shaida wa Lipavsky cewa ba za a yarda da munanan laifukan da Isra'ila ke aikatawa a kan fararen hula a Gaza ba.
Ya kuma jaddada bukatar tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba da kuma kai agajin jinƙai zuwa Gaza, majiyoyin suka jaddada.
Har ila yau Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar a ranar Litinin cewa, ministan harkokin wajen Belarus Sergei Aleinik zai isa Turkiyya domin wata ziyarar aiki ta kwana biyu a ranar Talata.
A yayin ziyarar ana sa ran Aleinik zai tattauna kan ci gaban yankin da kuma alakar da ke tsakanin kasashen biyu. Sannan zai halarci taron hadin gwiwa na hukumar tattalin arzikin Turkiyya da Belarus.
Isra'ila ta kai hare-hare ta sama da ta kasa a Gaza bayan harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Akalla Falasdinawa 10,022 da suka hada da yara 4,104 da mata 2,641 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza. Adadin wadanda suka mutu a Isra'ila ya kusan 1,600, a cewar alkaluman hukumomi.
Baya ga dimbin asarar rayuka da raba mutane da mhallansu, ana kuma fama da matsalar rashin kayan amfanin yau da kullum a Gaza, yankin da ke da mutum miliyan 2.3, sakamakon harin da Isra'ila ta kai musu.