Rufe iyakar Rafah da ta Kerem Shalom da ke kusa da ita, rufe muhimman hanyoyin kai kayan agaji ne, wanda hakan ke ƙara ta'azzara yunwa da ƙarancin magani a Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana ƙwace iko da ɓangaren Falasɗinu na kudancin Rafa da ke Gaza wanda ke da iyaka da Masar, wanda kuma yake da matuƙar muhimmanci wajen taimaka wa da fitar da waɗanda aka jikkata a yakin Gaza.
Me hakan ke nufi ga jama'ar Gaza?
A tsawon watanni bakwai da aka dauka ana yakin, mashigar Rafah da ke zaman iyaka daya tilo da ba a hannun Isra'ila take ba, ta zama mai matukar muhimmanci ga rayuwar Falasdinawa don zuwa wata duniyar. Tana bayar da damar kai kayan taimako da kwashe mutane, da ma daukar marasa lafiya daga asibitocin yankin da suka tabarbare.
Majiyoyin hukumomin bayar da agaji sun fada wa Reueters cewa an dakatar da kai kayan taimako ta iyakar Rafah.
Mahukuntan da ke kula da iyakokin da suke karkashin Falasdinawa sun bayyana cewa rufe mashigar Rafah kamar 'Hukuncin kisa ne ga jama'ar Gaza', musamman marasa lafiya da wadanda aka jikkata ta hanyar Rafah kadai ne suke iya fita daga kasar.
Hakazalika, an rufe mashigar da ta rage a bangaren kudu ita ce iyakar Kerem Shalom, wadda a baya-bayan nan aka yi amfani da ita wajen kai kayan taimako Gaza bayan harin makamin roka da Hamas ta kai, wanda ya kashe sojojin Isra'ila.
Kakakin Ofishin Ayyukan Jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, Jens Laerke ya ce matakin ya janyo rufe hanyoyi biyu na kai kayan agaji Gaza.
Mummunar yunwa, musamman a arewacin Gaza, na iya ta'azzara idan har aka dakatar da kai kayan agaji, in ji Hukumr Majalisar Dinkin Duniya da ke bayar da agaji UNRWA a wata sanarwa da ta fitar ta shafin X.
Shugaban hukumar samar da abinci ta MDD ya yi gargadi kan "mummunar yunwa" a arewacin Gaza da ke da mutane miliyan 2.3.
A baya Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana damuwa game da rufe iyakar Gaza da Masar, wanda zai iya yin babban tasiri wajen samar da magunguna da kai ma'aikatan lafiya zuwa yankin Gaza.
Me ya sa wannan iyake ke da muhimmanci??
Isra'ila ce ke iko da hanyoyin ruwa da sama na shiga Gaza da kuma mafi yawancin iyakokinta na ƙasa.
Ta kara tsaurara matakan da ta dauka a kan iyakokin tun bayan harin 7 ga Oktoba.
Bayan rufe iyakokin Isra'la, Rafah ta zama hanya daya tilo da Falasdinawa ke iya barin yankin, kuma mashigar ta zama mai muhimmanci wajen kai kayan agaji da kuma kwashe 'yan kasashen waje da marasa lafiya.
Qatar ta shiga tsakanin a tattaunawa tsakanin Masar da Isra'ila da Hamas, tare da jagorancin Amurka don bayar da dama a kwashe mutane daga yankin.
Tawagar farko ta mutanen da aka jikkata sun bar Gaza ne makonni uku bayan fara yakin a ranar 1 ga watan Nuwamba, sannan sai aka kuma kashe 'yan kasashen waje daga yankin.
Har zuwa ranar 7 ga Oktoba, Isra'ila ba ta da cikakken iko da mashigar Rafah, amma tana sanya idanu kan dukkan kai komon da ake yi a kudancin Gaza daga sansanin soji da ke Kerem Shalom. Wannan ne karo na farko da dakarun Isra'ila suka dawo iyakar Rafah tun 2005.