Sojojin Isra'ila na saka kayan matan da suka kashe a gidajensu, wasu na fasa ɗakunan girki suna sata a gidajen da aka gudu aka bari, wasu na hawa kekunan yaran Gaza da aka raba da gidajensu. Ana ta tambaya kan halayyar sojojin Isra'ila a Gaza.

Me ya sa sojojin 'da suka fi na ko ina tarbiyya a duniya' ke aikata aika-aika a Gaza?

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na yawan yabon sojojinsa da cewa su ne mafiya tarbiyya a duniya, tun bayan da a watan Oktoban bara ya aika su zuwa Gaza don kai hari.

Sai dai kuma, hotunan da ake yaɗa wa a shafukan sada zumunta na intanet irin su TikTok da Telegram da X na nuna yadda sojojin Isra'ila ke nuna munanan ɗabi'u, wadanda ba su yi kama da na nuna ƙwarewar soji ba.

A wasu daga cikin waɗannan bidiyoyin, an ga sojojin Isra'ila na saka kayan mata da fasa ɗakunan girki suna sace kayayyakin da aka bari, sannan suna hawa kekunan yara ƙanana a Gaza, a yayin da suka lalata gidajensu.

Wani bangare mai yawa na bidiyon da aka yada ya nuna sojoji suke cinna wa bututu wuta, kuma aka ga yadda gidaje ke ƙonewa, suna lalata kayan gwamnati da na makarantu, da kuma zagi da cin mutuncin Falasdinawa.

"Wasu daga ɗabi'un rashin tarbiyyar da sojojin Isra'ila suka nuna a bidiyon za su ɓata wa mutane da yawa rai, kuma su kunyata ƙwararrun sojoji da suka fahimci aiki da ladabi, kuma suka san me ake nufi da ladabi da hali mai kyau ga jami'in soji," in ji John D. Alternburg, Manjo Janar mai ritaya a rundunar sojin Amurka yayin tattaunawa da TRT Afirka.

Tsohon jami'in sojin na Amurka Manjo Janar din mai ritaya ya ce wasu daga wadannan bidiyo za su sanya a dinga yi wa dakarun sojin isra'ila kallo mara kyau "a cikin gida da ƙetare".

A yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare ba kakkautawa a Zirin Gaza da aka mamaye, ya zuwa yanzu ta kashe aƙalla Falasdinawa 31,000 da jikkata sama da 71,000, an ga yadda sojojin Isra'ila ke rushe gine-gine da isgilanci ga Falasdinawa.

Bidiyon da sojojin Isra'ika suka dinga yadawa da kansu sun nuna irin yadda suke yin abubuwa da yawa tun daga ayyukan soji zuwa lalata kayayyakin jama'a.

A watan da ya gabata, babban lauyan sojojin Manjo Janar Yifat Tomer-Yerushalm ya ui wani gargadin bazata a wata wasika dakarun da suka yi kutse kan su guji "aikata muggan laifuka"

"akwai bukatar a mayar da hankali sosai ga illar da nuna hali mara kyau zai iya raga kimar rundunar sojin." in ji Anltenburg.

Duk da rahotannin da aka samu na gargadin da manyan soji ke yi wa kananan, Sojojin Isra'ila a Gaza na ci gaba da lalata kayayyaki tare da cin fuska Falasdinawa.

Misali, a wani bidiyo an ga sojoji a kan kekuna. A wani kuma, an ga soja ya dauki darduman Sallah ya jefa su bandaki.

A wani bidiyon kuma, an ga soja na daukar bidiyon kamfen mata da aka bari a gidajen. A wani bidiyon da bai fita sosai ba ma, an ga soja na kokarin cinna wuta kan kayan abinci da sha don jefa Falasdinawa cikin yunwa.

A yayin da a baya ma an samu lokutan da sojojin isra'ila suka nuna rashin tarbiyya, yakin da suke yi a Gaza na zuwa ne a zamanin da ake da cigaban sadarwa.

Kasancewar sojoji na dauke da manyan wayoyin hannu, manyan na'urorin sadarwa, tazarar da ke tsakanin sadarwar zamani da filin daga ta kau.

Wannan ta'ada na sanya yaduwar hotuna d abidiyon da ba a tantance su ba - wadanda ka iya sauya tunanin jama'a game d ayakin da ake yi. Wannan na kuma kawo tsanantar munanar da yakin ya yi har zuwa dakunanmu.

Bayyanar wadannan bidiyo ya janyo tambayoyi game da halayyar sojojin Isra'ila a Gaza da kuma batun dokokin kasa da kasa da kare hakkokin dan adam.

Abubuwa masu tsoratarwa

"A yayin da a baya ma akwai irin yada wadannan bidiyo kamar a rikicin Rasha da Yukren, da ma a yayin da Amurka ta kutsa kai Iraki da Afganistan, amma wadannan bidiyon na Isra'ila sun fita daban saboda yadda suke da muni da nuna halin ko in kula ga rayuwar Falasdinawa fararen hula," in ji Waleed F, Mahdi, Mataimakin farfesa a Jami'ar Oklahoma yayin tattaunawa ta TRT World.

Mahdi ya kuma ce ba a yi mamaki ba yadda sojojin Isra'ila ke yada hotuna da bidiyon don jan hankali, wanda mafi yawancin lokuta hakan ya saba wa dokokin rundunar sojin Isra'ila.

Kwararren ya ce "Tabbas akwai wani mataki na nuna an fi karfin doka wand ake sanya wadannan sojoji nuna rashin tarbiyya. Akwai kuma wani dalili na tunani kan yaki da ke fayyace wadannan aika-aika."

Salo da tsari

Tasirin wadannan bidiyo ya wuce na tsakanin bakunan da kwakwalen jama'a kawai, ana tsammanin daukar mataka shari'a a nan gaba.

An samu bidiyo da dama da suka zama shaidar an yi kisan kiyashi da za a iya amfani da su a gaban kotu, ciki har wadanda Afirka ta Kudu ta gabatar a gaban Kotun Kasa da Kasa Mai Hukunta Manyan Laifuka, tana zargin Isra'ila d aaikata kisan kiyashi.

Farfesa Lisa Hajjar, wadda ta yi shuhura d abincikenta a Sashen Nazarin Zamantakewar Dan Adam a Jami'ar California, Santa Barbara, ta yi zurfi kan dokokin zamantakewa, yaki, 'yancin ɗan'adam da rikicin siyasa da al'amuran kasa da kasa a yau.

A tattaunawar da ta yi da TRT World, ta yi karin haske kan muhimmancin yadda sojojin Isra'ila ke ajje bayanan ta'annatin da suke yi.

Ta ce "Wannan abu da Isra'ila ke yi wani salo da tsari ne da ke cikin ayyukan gwamnatin Isra'ila inda a koyaushe ake zagin Falasdinawa da wulakanta su.

Wannan halayya, da ake murna yayin yin ta na sake tabbatar da tsana da kiyayya ga Falasdinawa wanda ya saba wa mutunta dan adam."

Dadin dadawa, game da batutuwan doka da shari'a kan wadannan bidiyo, bayyana ya sake bankado da irin rawar da shaufkan sadarwar yanar gizo ke taka wa wajen sauya ra'ayin mutane game da yakin da ake yi.

A yayin da dukkan duniya ta yi amo wajen mayar da martani kan wadannan bidiyo da hotuna, ana sake kiran da a yi gaskiya, ana bukatar da a dauki matakan magance wannan ta'annati.

Mahdi daga Oklahoma ya ce "Rashin tabbacin ko Isra'ila na daukan matakan ladabtarwa kan wadannan sojoji ko ba ta dauka, na bude kofar zato kan ko ayyukan na daidaikun mutane ne ko kuma tsara su aka yi a hukumance."

#