A wani sako da jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Dominique Hyde ta wallafa, ta bayyana cewa mutane 10,000 ne suka tsere daga Sudan don samun mafaka a makwabtan kasashe a kwanaki ukun da suka gabata.
Yayin da kazamin fada da ake gwabzawa a yankin Darfur ke kara tsanani tare da tilasta wa dubban 'yan Sudan barin matsugunansu, akwai bukatar a kara kaimi wajen rage radadi da kuncin rayuwa da miliyoyin 'yan kasar suka fada ciki, kamar yadda wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya MDD ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Cikin watanni shida an tilasta wa mutane miliyan shida yin kaura, wato kusan mutane miliyan daya ne suke tserewa daga gidajensu a kowane wata, suna fuskantar kunci rayuwa ," in ji Mamadou Dian Balde, babban jami'in yanki na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR).
Fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun da ke biyayya ga babban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) na Janar Mohamed Hamdan Daglo ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da mutum 9,000 tun daga watan Afrilu, a cewar wani rahoton MDD.
A cikin kusan mutane miliyan shida da suka yi gudun hijira, miliyan 1.2 daga cikinsu sun bar kasar, "mutane masu kima wadanda a yanzu suka tsinci kansu cikin yanayin bara" kuma rayuwarsu ta fada cikin ''garari baki daya,'' in ji jami'in na MDD.
Jami'ain ya yi gargadin cewa, yayin da hankalin duniya ya karkata zuwa ga yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, adadin mutanen da ke kaurace wa matsugunansu a Sudan ya kara yawa, yayin da dakarun RSF suka fadada kai hare-hare zuwa Nyala, birni na biyu da ke tsakiyar Darfur.
Mutane 10,000 sun kaura don samun mafaka a cikin kwanaki uku
Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniya a yankin, Dominique Hyde, ta wallafa labarin cewa ta ga abubuwan ban mamaki a kan iyakar Sudan a shafin sada zumunta na intanet a ranar Alhamis.
"Mutane 10,000 masu neman mafaka sun iso cikin kwanaki ukun da suka gabata," in ji ta.
Ana kan hankado mutane daga yankin Darfur zuwa kudu, da farko zuwa kasar Chadi a makonnin da suka gabata, yanzu kuma zuwa Sudan ta Kudu.
Sabbin sansanoni
Mamadou Dian Balde ya ce muhimmin abin da ya kamata a sa a gaba shi ne a kawo karshen yakin, yana mai cewa tattaunawar da ake yi a Jeddah ta kasar Saudiyya na bukatar ''a samu nasara wajen dakatar da wannan fadar.''
A sake komawa kan teburin tattaunawa tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a karshen watan Oktoba, kokarin sasanci na baya da aka yi, ya samar da takaitaccen sulhu da ba kai ga mutumta shi.
A halin yanzu, "dole ne mu rage radadi da kunci ('yan gudun hijirar) ta hanyar samar da kayan aiki ga wadannan mutanen da adadinsu ke ci gaba da karuwa," in ji shi.
Shirin Majalisar Dinkin Duniya na ba da agajin jin kai a watan Agusta ya bukaci a samar da kudade da yawansu ya kai kusan dala biliyan 1, inda aka yi hasashen kara samun wasu ‘yan gudun hijira miliyan 1.8 a karshen shekarar 2023.
Wannan shirin ya samu kashi 38 cikin dari na kudaden da ake bukata, yayin da "bukatu suka dada karuwa," in ji jami'in na MDD, yana mai cewa mafi yawan 'yan gudun hijirar suna kwarara zuwa yankunan da ke fama da talauci a Sudan ta Kudu da kuma kudancin Chadi, inda al'ummomin yankunan ba za su iya daukar yawansu ba.
Hakan na nufin Majalisar Dinkin Duniya za ta bukaci sake gina wasu sabbin sansanoni.
"Wannan shi ne abu na karshe da muke son yi, amma muna bukatar samar da sabbin sansanonin saboda yawan jama'ar suna kan iyakar kasar" kuma cikin mawuyacin yanayi." a cewar jami'in na Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kuma yi kira da a taimakawa al’ummomin yankin.
"Muna son ci gaba, dole ne mu saka hannun jari a wadannan wuraren domin idan kawai za mu ba da tallafi ga 'yan gudun hijira ne, hakan zai haifar da tashin hankali kuma tashin hankali na iya juya zuwa rikici."