Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 320,  ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,173 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,857, kuma an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashi ɓaraguzan gine-gine.

Mayaƙan Hezbollah sun kai hari da rokoki a yankin Tuddan Golan

Laraba, 21 ga watan Agusta, 2024

0811 GMT — Mayaƙan Hezbollah sun kai hari da rokoki a yankin Tuddan Golan

Sun kai harin ne kwana guda bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya gana da takwarorinsa na Masar da Qatar a yunƙurin baya bayan nan na tsagaita wuta a yaƙin Gaza, ko da yake Hamas da Isra'ila sun nuna cewa akwai tarin ƙalubale kan lamarin.

Wata sanarwa da hukumomi a Isra'ila suka fitar sun ce ana kula da lafiyar wani mutum ɗan shekara 30 da aka jikkata a harin na Tuddan Golan ranar Laraba. Wani gida ya kama da wuta, sannan ma'aikatan kashe gobara sun ce sun hana watsuwar gobarar ta hanyar toshe gas ɗin da yake yoyo bayan harin.

Hezbollah ta ce ta kai harin ne don yin martani kan hare-haren da Isra'ila ta kai a cikin Lebanon ranar Talata da daddare da ya kashe mutum ɗaya tare da jikkata mutum 19.

0230 GMT — An kama masu gangamin goyon bayan Falasɗinawa a Chicago

An kama gomman masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a wajen ƙaramin ofishin jakadancin Isra'ila da ke Amurka da kuma kan titunan birnin Chicago a dare na biyu na taron tsayar da 'yar takarar shugaban ƙasa ta jam'iyyar Democrat.

An yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, bayan da wasu daga cikin masu zanga-zangar – sanye da baƙaken tufafi kuma fuskokinsu a rufe – suka matsa kusa da shingen da 'yan sanda suka sanya don hana su isa wurin taron.

Wani mai zanga-zanga sanye da hular Chicago Bulls, wanda ya rufe fuskanrsa, ya yi kira ga masu zanga-zangar su "hana taron DNC."

Ƙungiyar da ta gudanar da zanga-zangar, wadda ba ta da alaƙa da gamayyar ƙungiyoyi fiye da 200 da suka yi zanga-zanga ranar Litinin ɗin da ta gabata, ta sanya wa zanga-zangar taken "Make it great like ’68," domin nuna irin zanga-zangar da aka yi a ƙasar don yin hamayya da Yaƙin Vietnam a yayin taron ƙasa na jam'iyyar Democrat na shekarar 1968.

An yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, bayan da wasu daga cikin masu zanga-zangar – sanye da baƙaken tufafi kuma fuskokinsu a rufe – suka matsa kusa da shingen da 'yan sanda suka sanya don hana su isa wurin taron./ Hoto: AFP

2030 GMT —Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a Qatar cewa bai kamata a ɓata lokaci ba game da amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Gaza a yayin da yake kammala ziyarar da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya.

"Lokaci yana da muhimmanci" domin a ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta, in ji Blinken a hira da manema labarai a filin jirgin saman Doha a yayin da yake shirin komawa Washington, yana mai ƙarawa da cewa Amurka ta yi watsi da "daɗaɗɗiyar" mamayar da Isra'ila ta yi wa yankin Gaza.

Ya ce Amurka da Masar da Qatar za su yi duk abin da ya kamata wajen ganin ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta amince da "yarjejeniyar da za ta kawo maslaha."

Hamas ta ce za ta yi biyayya ga yarjejeniyar farko wadda Biden ya gabatar sannan ta zargi Amurka da rashin gaskiya wajen aiwatar da ita. Hamas ta ƙara da cewa Isra'ila tana yin ƙafar-ungulu ga yarjejeniyar da aka gabatar tun da farko inda yanzu ta bijiro da sabbin buƙatu.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ranar Talata ya ce ƙasarsa ba za ta janye daga yankin Philadelphi (Saladin Axis) da ke kan iyakar Gaza da Masar da kuma yankin Netzarim ba, wanda ya raba Gaza zuwa gida biyu "komai zai faru."

Hamas ta ce wannan sabuwar buƙatar da Netanyahu ya bijiro da ita abu ne da ba zai yiwu ba.

Blinken (Tsakiya daga hagu) ya gana da Ministan Harkokin Wajen Qatar Mohammed bin Abdulaziz al-Khulaifi (Tsakiya daga dama) a Doha ranar 20 ga Agusta, 2024. / Hoto: AFP

2000 GMT — An zargi Netanyahu da kawo matsala a yarjejeniyar tsagaita wuta

Wasu mambobi da ke cikin tattaunawa da za ta kai ga sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma tsagaita wuta sun zargi Netanyahu da yin ƙafar-ungulu a shirin da gangan bayan ya shaida wa wasu taruka na Tikva da Gvura cewa "Isra'ila ba za ta fice daga yankin Philadelphi da na Netzarim ba komai zai faru," a cewar kafar watsa labarai ta KAN.

"Netanyahu ya yi kalaman ne domin kawo tarnaƙi a tattaunawar, babu wata shakka game da hakan," kamar yadda wata majiya ta shaida wa KAN.

"Firaminista ya sani cewa muna cikin mawuyacin yanayi inda muke aiki tuƙuru domin samar da mafita game da yankunan Philadelphi da Netzarim gabanin taronmu a gaba."

"Ya san cewa ana samun ci gaba — amma ya yi waɗannan kalamai da suka ci karo da waɗanda aka amince da su da masu shiga tsakani," in ji majiyar.

#