Ya bayyana cewa Jihar Kano kaɗai na da kusan malamai 25,000 da ba su da cancantar koyarwa, inda ya ce zuwa yanzu an mayar da kusan 8,000 daga cikinsu ƙwararrun malamai ta hanyar ƙoƙarin gwamnatin jihar da TRCN.
Josiah Ajiboye, Shugaban Majalisar Rajistar Malamai ta Nijeriya (TRCN), ya ce kusan malamai 300,000 daga cikin malamai 700,000 da ke Nijeriya ba su da ƙwarewar koyarwa.
Ya bayyana cewa Jihar Kano kaɗai na da kusan malamai 25,000 da ba su da cancantar koyarwa, inda ya ce zuwa yanzu an mayar da kusan 8,000 daga cikinsu ƙwararrun malamai ta hanyar ƙoƙarin gwamnatin jihar da TRCN.
An tura su Cibiyar Malamai ta Nijeriya (NTI), kwalejojin ilimi da kuma shirye-shiryen Difloma na Ilimi ga waɗanda suka kammala karatun jami’a.
Ajiboye ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wani taron tattaunawa mai taken “Koyarwa cikin ’yanci: Ƙarfafa malaman Nijeriya domin tunkarar ƙalubalen ƙarni na 21”, wanda aka shirya domin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2017.
Ya ce siyasantar da harkar ilimi da gwamnonin jihohi da sauran masu riƙe da mukaman siyasa ke yi ce babbar hanyar shigar malaman da ba su da cancanta cikin tsarin.
Ya ce koyarwa sana’a ce da ke buƙatar shiri da ƙwarewa, don haka bai kamata a mayar da ita sana’ar da kowa zai iya shiga ba.
A cewarsa, wasu ’yansiyasa kan ba mutanen da ba su samu aikin yi ba aikin koyarwa domin kawai su faranta musu rai.
Ajiboye ya kuma koka kan rashin kyakkyawan yanayin aiki da malamai ke fuskanta a Nijeriya, inda ya ce ana jinkirta musu karin girma, kuma a wasu lokuta idan an yi musu karin girma, ba a tanadi kuɗin aiwatar da shi ba.
Ya misalta Jihohin Oyo da Osun, waɗanda a baya suka yi fice wajen jarabawar ƙasa, amma yanzu sakamakonsu ya ragu sakamakon rashin ƙarfafa wa malamai gwiwa.
Ya kuma ce wasu jihohi sun taɓa bin malamai bashin albashi na tsawon watanni takwas.
Dangane da matsalar rashin tsaro da ta shafi malamai, Ajiboye ya ce an kashe malamai sama da 611 a Arewa maso Gabas tun bayan fara hare-haren Boko Haram a 2009, yayin da wasu 19,000 suka rasa matsugunansu.
Ya ce hare-haren ’yan ta’addan sun kawo cikas ga harkokin ilimi a yankin, lamarin da ya tilasta wa malamai da dama barin yankin domin tsira, wasu kuma suka koma wasu jihohi ko ƙasashen makwabta.

