Wannan ne karo na takwas da dan kasar Ajentina Lionel Messi, wanda yanzu yake murza leda a Inter Miami, ya lashe gasar Ballon d'Or.
Shahararren dan kwallon kafar duniya Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d'Or karo na takwas a bikin da aka yi a a Paris ranar Litinin.
Dan kasar Ajentina ya cika burinsa na rayuwa lokacin da ya jagoranci tawagar kasarsa wajen lashe Gasar cin Kofin Duniya da aka gudanar a Qatar a 2022 bayan ya kwashe shekaru ba su ci kofin ba.
'Yar kasar Sifaniya Aitana Bonmati ce ta lashe kyautar Ballon d'Or rukunin mata bayan ta jagoranci kasarta wajen cin Kofin Gasar Kwallon Kafar Mata ta Duniya da aka yi a watan Agustan da ya gabata.