Kasar Afirka ta Kudu ce ta shigar da karar kan cewa Isra'ila ta karya doka ta hana kisan kare-dangi ta Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1948, wadda aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu da na kisan kare-dangi a Turai.
Kotun hukunta manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya ICJ ta umarci Isra'ila da ta dauki dukkan matakan da za ta iya dauka wajen dakile aikata kisan kiyashi a Gaza.
A umarnin da kotun ta bayar a ranar Juma'a a ta kuma umarci Isra'ila da ta saukaka ayyukan jinkai a yankin da aka yi wa kawanya.
Kotun ICJ ta ce tana da hurumin yanke hukunci kan matakan gaggawa, tana mai cewa ba za ta yi watsi da batun kisan kare-dangi ba kamar yadda Isra'ila ta bukata.
Kazalika ta bayyana Falasdinawa a matsayin wata al'umma da ke da kariya a karkashin yarjejeniyar kisan kare-dangi, tana mai jaddada cewa ta amince da hakkin Falasdinawa a Gaza na samun kariya daga ayyukan kisan kare-dangi.
A ranar 29 ga watan Disamba ne kasar Afirka ta Kudu ta shigar da kara a gaban kotun ICJ inda ta bukaci a hukunta Isra'ila saboda harin da take kaiwa Gaza ya sabawa yarjejeniyar kisan kare-dangi..
Daga cikin bukatun matakan da Afirka ta Kudu ta nema, akwai bukatar gaggawa na dakatar da Isra'ila daga kai mumunarn hare-hare wanda ta sanadiyar kashe Falasdinawa sama da 26,000, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.
Haka kuma kasar ta bukaci kotun ICJ ta ba da umarni a hukumance saboda gaggawar lamarin.
Bayan kammala sauraren karar a ranakun 11 zuwa 12 ga watan Janairu, kotun ta fara tattaunawa bayan ta yi nazari kan abubuwan da bangarorin suka gabatar da kuma shaidu.