Gwamnatin jihar ta ce hukuncin ya tabbarar da adalci ga waɗanda lamarin yarutsa da su da iyalansu, waɗanda suka jure wahala da tashin hankali a lokacin garkuwa da su.
Babbar kotun jihar Bauchi ta yi wa mutum uku ɗaurin shekara 21 kan haɗin baki na aikata laifi da garkuwa da mutane da sace mutane.
Alƙali Farouq Sarki na babban kotun ya yanke hukuncin ne ranar Laraba bayan shekara biyu da aka yi ana sharia kan mutane 11 da ake tuhuma.
An fara shari’ar ne a watan Maris na shekarar 2024, biyo bayan nasarar da rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta samu a watan Disambar 2023, a lokacin ta kama wasu da ke da hannu wajen sace yara daga jihar Bauchi.
An yi zargin cewa an kai yaran kudu maso gabashin ƙasar ne inda aka sayar da su.
Yaran, waɗanda dukkansu shekarunsu suke ƙasa da 10, sun ɓata ne a lokuta daban daban tsakanin shekarar 2016 zuwa shekarar 2023. Daga baya ne ‘yansanda suka ceto su kuma suka haɗa su da ‘yanuwansu.
Da yake gabatar da hukuncin, Alƙali Sarki ya yi wa ko wanne daga cikin mutum ukun da kotu ta smau da laifi ɗaurin shekarar 21, ba tare da zaɓin tara ba.
An sami biyu daga cikinsu da laifi ne kan tuhume-tuhume 21, yayi da aka samu na ukun da laifi kan tuhume-tuhume uku.
Saura mutum takwas da ake zargi an sake su kuma an wanke su daga zargi.
Babban lauyan gwamnatin jihar, Sabi’u Gumba, ya ce hukuncin ya tabbatar da adalci ga waɗanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu, waɗanda suka jure wahala da damuwa a lokacin da aka sace su.
“Ka raya cewa an saka iyaye cikin matsalar rashin sanin inda ɗansu yake na tsawon lokaci. Babban nauyi ne,” in ji Gumba.
“Waɗannan mutane sun kama yara bakwai zuwa tara. Idan ka kwatanta nauyin abin da suka aikata da ɗaurin da aka yi musu, za ka yarda da ni cewa ɗaurin ya cancanta.”
Ogbuchi Ben, wanda shi ne lauyan na uku daga cikin waɗanda aka gurfanar, ya ce lauyoyin da ke kare waɗanda aka gurfanar za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
“Tabbas za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yi wa mutum na ukun da aka gurfanar. Babu hujjar samunsa da laifi,” in ji shi.
Florence Bwala, lauyar mutum na biyun da aka gurfanar, ta ce wanda take karewa na da ‘yancin iya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
“Wanda aka samu da laifin na da ‘yancin ɗaukaka ƙara, kuma wannan hukuncin nata ne. Idan tana so ta wuce Kotun Ɗaukaka Ƙara, za mu wuce Kotun Ɗaukaka ƙara,” in ji ta.
Sai dai kuma, gwamnatin jihar ta yi kira ga iyaye da masu kula da yara da ma al’ummomi su mayar da hankali kuma su ɗauki matakan da suka dace domin kare yara daga sata da sauran nau’o’i na bautarwa.