Kazalika an tuhumu fararen-hula biyu da wani dan sanda da laifin boye yunkurin cin amanar kasa da kuma hada baki wurin kifar da gwamnati.

Kotu ta daure sojojin da suka yi yunkurin kifar da gwamnati a Gambia

Wata babbar kotun Gambia ta yanke hukuncin daurin shekara 12 ga wasu sojoji da suka jagoranci yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasar Adama Barrow a bara.

A watan Janairu aka tuhumi sojojin takwas da laifin cin amanar kasa da hada baki don kifar da gwamnati ranar 21 ga watan Disambar 2022 lokacin da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar mai mutane fiye da miliyan 2.5.

Kazalika an tuhumu fararen-hula biyu da wani dan sanda da laifin boye yunkurin cin amanar kasa da kuma hada baki wurin kifar da gwamnati.

Sai dai kotun ta wanke mutum bakwai, ciki har da fararen-hula biyu da kuma wani bannan soja daya, a yayin da ake tsaka da shari'ar.

An tuhumu wani babban soja, Sanna Fadera, wanda shi ne ya jagoranci yunkurin juyin mulkin, da laifin cin amanar kasa. Sai dai an wanke karin sojoji uku da tun da farko aka zarge su da laifi.

#