Reshen hukumar EFCC na Kaduna ne ya shigar da Jesse Joshua Kassah kara a gaban kotu bayan an kama shi a yankin Karji na jihar kan zargin damfara.
Hukumar da ke Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Kasa, EFCC, ta ce kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu kan samun shi da laifin yi wa rundunar sojin Amurka sojan gona.
Mai Shari’a Darius Khobo na Babbar Kotun Kaduna ne ya yanke masa hukunci bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa guda daya tal da ake zarginsa da aikatawa.
Bayan yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu, Mai Shari’a Khobo ya ba shi zabin biyan tarar naira 150,000.
Sannan alkalin ya bayar da umarnin kwace wayar Kassah wato Samusng Galaxy A02 wadda ita ya yi amfani domin aikata laifin ga gwamnatin Nijeriya.
Reshen hukumar EFCC na Kaduna ne ya shigar da Jesse Joshua Kassah kara a gaban kotu bayan an kama shi a yankin Karji na Kaduna kan zargin Damfara.
Hukumar ta ce Jesse na amfani da sunan wani sojan Amurka mai suna Devaun Smith Wayne domin damfarar jama’a.
Zamba cikin aminci da yaudara na daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta EFCC ke yaki da su a Nijeriya.
Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta EFCC ta kama wani matashi wanda ake zargi da yi wa matar Sarkin Bichi zamba cikin aminci ta naira miliyan 20.