A watan Satumba, an kai wani mummunan hari kan jirgin ruwa a "Tumbuktu" a yayin da yake tafiya a kan Kogin Niger na kasar Mali wanda ya razana fasinjojin jirgin. Shaidun gani da ido sun bayyana yadda harin ya afku da sadaukarwar ta tsawon m

Kisan kiyashin da aka yi a wani jirgin ruwa a Kogin Niger da ke Mali

Fasinjojin Timbuktu, jirgin ruwan da ke kai komo a Kogin Niger a arewacin Mali, sun saba da jin karar harbe-harbe daga gabar kogin a yayin da suke tsaka da tafiya.

Amma a ranar 7 ga Satumba, sun yi hanzarin gano wani abu da ba su saba gani ba na afkuwa.

Karar fashewar da ta tirsasa fasinjoji bugun bangon jirgin a wannan rana ta biyo bayan harbi da bindiga.

Zai hallaka rayuka da dama tare da barin jirgin ruwan - wanda yake hada garuruwan Mali waje guda d ake gabar kogin da ke da nisan daruruwan kilomitoci, sahara da busassun dazuka.

Har a kasar da ta saba da ganin kisan mutane da dama a lokaci guda saboda hare-haren 'yan bindiga, 'yan daba masu tsare kawunansu, sojoji ko mayakan kasashen waje, an kai hari mummuna a kan ruwa a wajen da ke da nisan kilimota 20 daga garin Bamba.

Babu wanda ya san wanda ya kai harin makamin roka na tsawon mintuna 15, an yi ta ruwan harsashai da ɓarin wuta kan ɗaruruwan fasinjojin, kuma babu tabbacin za a iya gano wanda ya yi wannan aika-aika.

Shaidu 12 sun amince su bayyana wa AFP yadda abun ya afku. Sun bayyana ta'addancin da yadda faru, da kuma irin sadaukarwar da sojoji suka yi ga rayuwar wadanda lamarin ya rutsa da su.

Tun 2012, yankin Sahel ya zama wajen afkuwar ibtila'o'i da ba a rawaito su, kuma ba tare da wasu bayanai na hotuna ba.

Wadannan bayanai na kara fitar da yadda wannan kisan kiyashi da ba a san wadanda suka aikata shi ba.

Daya daga cikin wadannan shaidun Alhadj M'bara, da ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin jaruman 'Tumbuktu' -- jirgin mai kalar fari da shudi, da wata tutarsa tsohuwa, kuma dauke da tambarin hukumar 'Societe Malienne de Navigation (Comanav)'.

M'bara, wanda ke da shekaru sama da 60, ya zauna a kan tabarma a tsohon gidansa a garin Timbuktu, inda yake bayar da labarinsa.

Ya ce kamar sauran mutane, shi ma yana sayar da 'yan kayayyakin amfani a gidaje ne a kan jirgin da ke yin tafiya ta kwanaki.

Yana da wajen da ya saba tsayawa a cikin jirgin, wanda nan ne asubahin 7 ga Satumba ta riske shi.

Akwai mutum tsakanin 500 zuwa 1,000 a cikin jirgin, duk da cewar an yi shi ne da nufin dinga ɗukar mutum 300.

Kusan lokacin karin kumallo ya yi, kuma fasinjoji sun damu matuka.

"Tun lokacin da muka bar Timbuktu, mun samu jita-jitar wai za a kai wa jirgin ruwan hari," in ji dattijon.

Ta'azzarar rikici

Tsawon makonni, lamarin na ta'azzara tsakanin masu dauke da makamai na arewaci da suka hada da kungiyoyin mayaka, 'yan ware da kuma sojoji.

Kungiyar GSIM da ke da alaka da Al Qa'eda ta tsare hanya a Timbuktu, kuma duk wasu matafiya daga ko zuwa garin na zama cikin taskun fuskantar hari.

Kafin kai harin, kogin ya bayar da hanyoyin samun kariya daga harin.

A ranar 1 ga Satumba, an kashe wani matashi sakamakon harin roka a ganin hukumar Comanav.

Kwanaki biyar bayan hakan, wasu da ke cikin jirgin ruwa suka gargadi matafiya a hanyar Gao kan yiwuwar kifar da su.

A matsayin matakan kar ta kwana, an shirya za a dan tsaya a wannan dare a Bamba, tsakanin garuruwan Gao da Timbuktu.

Da misalin karfe 9:00, washe gari, a nisan kimanin kilomita 15 bayan an wuce Bamba, sai jirgin ruwan ya shiga wata kwana mai gargada.

Wata ɗaliba Aicha Traore tana daukar hotuna a kan gada yayin da wata motar a kori kura ta duro kai tsaye, kamar yadda wani ganau ya bayyana.

Ta ce "Wasu mutanen sun ce watakila motar Sarkin kauyen ce."

Akwai sojoji a kan jirgin ruwan, sai ita da wasu suka je suka sanar da su.

Abun tambaya a nan shi ne ko kasancewar sojoji a cikin sa ne ya sanya aka kai wa jirgin harin, idan haka ne to wa aka kai wa harin kenan.

"Sannan ne harbin ya fara" in ji M'bara.

Sojoji sun umarci mutane da su kwanta a cikin jirgi.

"Wasun mu sun kwanta a kan mu don ba mu kariya," in ji Abdoulrazak Maiga, dalibi mai shekara 19.

Kirga gawarwaki

A baya ma an taba kai wa jirgin ruwan Timbuktu hari, kamar yadda M'bara ya bayyana.

Ya ce "a wannan karon abun ya sha bam-bam."

"Muna tsaka da tafiya, kawai sai muka ji hari da makamin roka", harin ya zo daga wani karamin jirgin ruwa da ke kusa da namu.

M'bara ya kara da cewa "Daga nan kuma, sai kowa ya koma ta kansa, kowa ya koma ga Allah."

Sojojin sun yi kokarin mayar da martani, amma musayar wutan da ake yi ta kassara su, saboda suna da kananan makamai, maharan na da makaman roka.

Mai aikin jirgin ya ce makaman roka uku ne suka fado kan injin jirgin nasu.

Sai wuta ta kama wadda ta bazu a cikin jirgin.

Fatoumata Coulibaly mai kanti a cikin jirgin ya ce "na mika dan karamin ɗan'uwana ga wani, ina ni kuma na tsuduma cikin ruwa ba shiri."

"Sai na fada masa ya miko min dan karamin ɗan'uwana -- Na iya yin ninƙaya zuwa gaba tare da shi, amma dukkan kayanmu suna cikin jirgin, har da kayanmu da takalmanmu."

A yayin tsoron, Aessata Issa Cisse, wata fasinja, ta rabu da 'yarta.

"Ban samu labarinta ba -- Na dinga bincike cikin kosawa, ban sani ba ko tana raye," ta shaida wa AFP.

Matukin jirgin ya yi kokarin isa gaba.

Mazauna ƙauyen da ke gabar ruwan ne suka fara kawo dauki ga jama'a.

Bayan wasu awanni, sojoji da wasu farar fata kimanin 15 dauke da bindigogi, watakila daga mayakan Wagner sai suka isa wajen.

Maharan sun gudu, amma hanyar na da hatsari idan aka ce za a kwashe mutanen da suka kubuta, wadanda suka shafe dare karkashin kulawar sojoji a gaban jirgin da ya ƙone.

An binne wadanda suka mutu a wajen.

Ba a san adadin asarar rayyka da dukiya da aka yi ba. Dalilai da dama ne suka hana a iya gano wannan adadi ko alkaluma; nisa da munin yankin, rashin sadarwar zamani a wajen, rashin hanyoyin isar da bayanai da tsoron yin magana da bayar da sheda.

Kungiyoyi masu zaman kansu da Majalisar Dinkin Duniya na yawan ajiye bayanan kisna kiyashi da ake yi a yankin bayan bayanan baki da suka samu daga shaidun gani da ido.

A 'yan shekarun nan an gaza isa ga yankin ma kwata-kwata, yayin ta'azzarar yanayin siyasa da na tsaro.

Cikin 'yan awanni labarin hari kan jirgin ruwan ya mamaye ko ina, tare da hotunan jirgin yana cin wuta wand ayake ta yawo a shaukan sada zumunta.

A wannan yammaci shugabannin soji na Mali suka fitar da bayanai game da lamarin.

Gwamnatin ta tabbatar da mutuwar farar hula 49 da sojoji 15 sakamakon harin na jirgin ruwa da kuma wani hari da aka kai wa cibiyar sojoji a Bamba.

Juriya

Sojojin sun bayyana cewa kungiyar GSIM ta dauki alhakin kai hare-haren guda biyu. AFP kawai sun iya gano burbushin kungiyar na duakar nauyin kai hari kan cibiyar soji, amma ba su fadi ko su suka kai wa jirgin ruwan ba.

Daga baya kuma, mahukunta sun alakanta hare-haren da sauran ayyukan ta'addanci na kungiyoyn da ke dauke da makamai.

Kungiyoyin da ke goyon bayan sojoji 'yan juyin mulki a shafukan sada zumunta na yanar gizo sun dora laifin hari kan jirgin ruwa a kan 'yan tawayen Tuareg, sai suke fake wa da GSIM.

"Ruruwar rikici a arewaci - gamayyar 'yan ta'adda da mayaka masu neman 'yanci duk suna fafatawa," ne babban kanun labaran jaridar I'Essor ta ranar 11 ga Satumba.

Wani jami'i daga Kungiyar Gwagwarmayar Azawad (CMA) - babban kawancen 'yan ware - ya musanta hannun su, inda ya yi jawabi kan sharadin kar a bayyana sunan sa.

Kamar yadda yake a mafi yawancin lokuta, shaidun gani da ido ma sun musanta adadin da gwamanati ta ce sun mutu sakamakon harin.

Wadanda suka kubuta da dama sun ce an binne mutane 111 a ramuka guda uku daban, na mata, maza da yara kanana.

Wannan adadi bai hada da wadanda suka kone ko dilmiye wa a ruwa ba.

Babu wani bayani da ake da shi kan gano mutanen da suka mutu, ko kuma ma an gano wani din ma.

Shugabannin sojin sun ayyana zaman makoki na kwanaki uku.

An soke bukukuwan da aka shirya yi na Ranar 'Yancin Kan Mali ta 22 ga Satumba, aka bayar da umarnin tamakawa wadanda lamarin ya rutsa da su da kudin gudanar da bukin.

Shaidu sun bayyana cewa sun samu kudaden tallafi daga gwamnati da ya kai kusan dalar Amurka 400.

Kotunan sun sanar da fara gudanar da bincike, kuma shugaban soji Assimi Goita ya tabbatar da cewa wannan harin da wasun su ma, ba za su wuce haka kawai ba tare da hukunta maharan ba.

Duk da zargi, amma ba a iya gano su waye suka kai harin ba. Babu wani daga masu bayar da shaida da ya bayyana ko su waye za su iya kasnacewa wadanda suka kai harin.

Kwana daya bayan afkuwar ibtila'in, da rana tsaka, wani karamin jirgin ruwa ya dauki wadanda suka kubuta -- kusan mutane 400 -- zuwa garin Gourma-Rharous, bayan tafiyar 'yan kilomitoci.

A nan suka dan jira a wasu ajujuwa na kwanaki da dama kafin a kai su gidajensu.

Daliba Traore ta tuna da irin ihun da wadanda suka kubuta suke ta yi.

Ta ce ita ce kadai ta kubuta daga cikin wadanda suke zaune a daki daya a cikin jirgin.

"Abunda ya same mu shi ne ikon Allah," ta ce yayin da tame dan ajiyar zuciya, amma da karfin hali, tana zaune a gidanta na kasa a garin Timbuktu.

M'bara, wanda ya kubutar da dan sa ta hanyar kama hannunsa ya ja shi cikin ruwa, na fatan za a dawo da zirga-zirga a kogin.

Ya ce "Zama haka ba a yin komai ba mafita ba ne."

#