“Daga arewa zuwa kudu, sun raba jama’ar Gaza da muhallansu, sun jefa musu bam ta sama da ruwa da kasa da ta ko ina. Abin da suke son yi shi ne kawar da Falasdinawa daga kasar,” in ji Shugaba Erdogan.

Kasashen Yamma ba su kallon turjiyar Falasdinawa a matsayin kare kai: Shugaba Erdogan

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, ga dukkan alamu shugaban kasar Jamus Steinmeier da shugabar gwamnati Scholz sun damu ne kadai da kungiyar Hamas, inda suka danganta abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, kawai da harin da Hamas ta ka kai a ranar 7 ga watan Oktoba, maimakon daukar lamarin a matsayin wani abu guda.

“A martanin da muka mayar, mun bayyana musu karara cewa muna daukar Isra’ila kasar ‘yan ta’adda” kamar yadda Shugaban Turkiyya Erdogan ya bayyana a lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a lokacin da yake cikin jirgi yake hanyar komawarsa gida daga Jamus a ranar Asabar, inda ya hadu da jami’an Jamus domin tattaunawa kan hare-hren da Isra’ila take kaiwa Gaza da kuma dangantakarta da Turkiyya.

Ya tuna musu da cewa an kashe yara da mata da dattawa 13,000 a Falasdinu, yayin da aka gabatar da mutuwar 100-200 a bangaren Isra’ila a matsayin a takaice.

Munafunci

Erdogan ya soki batun cewa abin da Isra'ila ke yi ya dace da kuma goyon baya mara iyaka daga kasashen yamma da Isra’ilar ke samu.

Daga karshe dai suna kallon abin da Isra'ila ke yi a matsayin kare kai amma ba sa kallon tsayin daka na Falasdinu a matsayin kare kai,” in ji shi.

Masu cutar daji da aka kai Turkiyya

An kwashi masu cutar daji da dama daga Gaza inda suka tafi Turkiyya a ranar Laraba daga filin jirigin sama na soji da ke arewa maso gabashin Masar.

Tuni aka tabbatar da soma duba masu cutar 27 daga Gaza wadanda aka kai Turkiyya, kuma an soma yi musu magani, kamar yadda wata sanarwa da Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya bayyana a ranar Asabar.

Kan wannan batun Shugaba Erdogan ya bayyana cewa “Muna daukar matakai da dama a Gaza, inda muka fi mayar da hankali kan batun tsare-tsaren kiwon lafiya.

Zuwan marasa lafiya masu cutar daji 27 kasarmu kaso kadan ne na wannan matsalar; adadin marasa lafiyar ya fi hakan yawa. Akwai wasu daruruwan a halin yanzu da ke bukatar tiyata.” “Asibitocinmu na nan. Ku bari mu kwashe su, muddin sun amince da hakan. Bari mu kawo su asibitocinmu, mu ba su kulawa mu kuma mayar da su,” in ji shi.

Kai agaji Gaza

Shugaba Erdogan ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya mai dorewa, yana mai cewa "Mataki mafi dacewa ga Gaza shi ne tsagaita bude wuta nan take, kuma fifikonmu shi ne samar da zaman lafiya mai dorewa tare da tsagaita bude wuta. Da zarar an cimma tsagaita bude wuta, za mu yi duk abin da ya kamata domin Isra'ila ta biya diyya kan baranar da ta yi," in ji shi.

"Za mu yi iya kokarinmu domin sake gina abubuwan da aka lalata a Gaza, da kuma mayar da hankali wurin sake gina makarantu da asibitoci da kayayyakin ruwa," in ji shi.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata ne Gazata shiga tsananin bukatar agajin jinkai, "Barin Iyakar Rafah a bude na da matukar muhimmanci. Ta kasance wata hanyar rayuwa ga mutanen Gaza, wadda za ta ci gaba da raya fararen hula da rayukan da ba su ji ba su gani ba," in ji shi.

#