Dakarun Isra'ila sun ci gaba da luguden wuta a Gaza ranar Juma'a jim kadan bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta da suka kulla da Hamas ya kare.
Gwamnatin Falasdinu da ke Gaza ta dora alhakin "laifukan yakin da Isra'ila take ci gaba da aikatawa" a kan kasashen duniya, a yayin da dakarun Isra'ila suka ci gaba da kaddamar da hare-hare a Gaza bayan karewar wa'adin yarjejeniyar tsagaita.
"Rundunar sojin Isra'ila da ke mamaya ta sake kaddamar da yaki mai muni a kan al'ummar Falasdinu da ke Zirin Gaza,” a cewar wata sanarwa da ofishin watsa labarai na gwamnati da ke Gaza ya fitar ranar Juma'a da safe.
Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare a gidaje da dama da kuma kan fararen-hula a Gaza, in ji ofishin na watsa labarai, inda ya jaddada cewa: “Kasashen duniya ne za su dauki alhakin laifukan yakin da Isra'ila ke ci gaba da aikatawa a Zirin Gaza.”
Hukumomin lafiya a Gaza sun bayyana cewa luguden wutar da Isra'ila take ci daga da yi a yau ya kashe Falasdinawa 32.
“Kasashen duniya, musamman Amurka da shugabanta Joe Biden da Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken, su ne da alhakin laifukan mamaya da na yakin da Isra'ila take aikawa a kan fararen-hula da kananan yara da mata a Gaza,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa: “An keta dokokin yaki da na kasashen duniya game da jinkai. Kasashen duniya sun bai wa Isra'ila damar ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza.”