Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 124 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,585 sannan suka jikkata mutum 66,978, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin.

Kai-tsaye: Yawan wadanda suka mutu a Gaza ya kai 27,708 yayin da ake tsaka da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

1146 GMT –– Yawan wadanda suka mutu a Gaza ya kai 27,708 yayin da ake tsaka da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Akalla Falasdinawa 27,708 aka kashe a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce adadin na baya-bayan nan ya hada da mutuwar mutane 123 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, yayin da adadin mutane 67,147 suka samu raunuka a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.

0623 GMT Ƴan majalisar Amurka sun yi watsi da kudirin tallafa wa Isra'ila da dala biliyan 17.6

Majalisar Wakilan Amurka ta yi watsi da wani kudiri a ranar Talata wanda zai bai wa Isra’ila tallafin dala biliyan 17.6.

Ƴan Jam’iyyar Democrats 166 da ƴan Republican 14 ne suka yi watsi da kudirin inda, wanda hakan ya sa mutum 250 waɗanda suka goyi bayan kudirin gaza samun goyon bayan kaso biyu cikin uku kafin gabatar da kudirin.

Da dama daga cikin waɗanda suka yi watsi da wannan kudirin sun kawo batun hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Gaza, inda ƴan majalisar suka yi kira da a kare haƙƙin bil’adama.

0045 GMT — Saudiyya ta jaddada cewa ba za ta shirya da Isra'ila ba sai ta tsagaita wuta a Gaza

Saudiyya ta shaida wa Amurka matsayinta na cewa ba za ta kulla huldar diflomasiyya da Isra'ila ba, matukar ba a amince da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta a kan dokokin 1967 ba, da kuma sanya Gabashin Birnin Kudus, a matsayin babban birninta, kuma har sai Isra'ila ta dakatar da kai wa kan Gaza da aka yi wa ƙawanya hare-hare, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya a wata sanarwar.

A ranar Talata, mai magana da yawun Fadar White House John Kirby ya ce gwamnatin Biden ta sami martani mai kyau cewa Saudiyya da Isra'ila a shirye suke su ci gaba da tattaunawar daidaitawa.

Ma'aikatar ta ce Masarautar ta fitar da sanarwar ne domin tabbatar da tsayuwarta tsayin daka ga Washington kan batun Falasdinu bisa la'akari da kalaman da ake dangantawa da Kirby.

0303 GMT — 'Yan Houthi na Yemen sun harba makamai masu linzami kan jiragen ruwa a Bahar Maliya

Kungiyar Houthi ta Yemen ta harba makamai masu linzami guda shida kan wasu jiragen ruwa na kasuwanci guda biyu, inda rahotanni suka ce sun yi ɓarna kadan ga daya daga cikin jiragen, in ji rundunar sojin Amurka.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta Amurka ta fitar ta ce, mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun harba makami mai linzami guda shida (ASBM) daga yankunan da Houthi ke iko da Yemen zuwa Tekun Maliya da Tekun Aden.

An harba uku daga cikin makami mai linzamin kan jirgin MV Star Nasia ne, wani jirgin ruwan dakon kaya mai dauke da tutar Tsibirin Marshall mallakin Girka kuma mai sarrafa kansa, in ji rundunar sojin.

Sauran makamai masu linzami guda uku da alama sun nufi kan MV Morning Tide ne, wani jirgin dakon kaya mallakin Birtaniya mai tutar Barbados, amma sun fashe a cikin Bahar Rum ba tare da yin lahani ba.

#