Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 118 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,019 sannan suka jikkata mutum 66,139, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin.
1049 GMT — Yawan mutanen da aka kashe a Gaza sun wuce 27,000
Akalla mutum 27,019 ne suka mutu a cikin kusan watanni hudu na yakin da Isra'ila take yi a Gaza, in ji Ma'aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Wata sanarwar ma'aikatar ta kuma ce an jikkata mutum 66,139 tun bayan ɓarkewar yaƙin na Gaza ranar 7 ga watan Oktoban 2023,
0744 GMT — Isra'ila ta kama gomman Falasɗinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Sojojin Isra'ila sun raunata wasu Falasdinawa biyu tare da kame akalla wasu 37 yayin wani jerin sabbin kutse da suka yi a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye, a cewar majiyoyin lafiya.
Majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an harbi Falasɗinawa a yayin da ake arangama da sojojin Isra'ila a birnin Tubas da ke arewaci. An harbi daya daga cikinsu a gadon baya daya kuma a kafa.
A cewar majiyoyin lafiya, dakarun Isra'ila sun dirar wa Tubas tare da kama Falasɗinawa biyu, lamarin da ya jawo yin arangama da gomman Falasɗinawa.
Sojojin Isra'ila sun yi amfani da harsasai da kuma barkonon tsohuwa, wajen tarwatsa Falasdinawan da ke jifan dakarunsu da duwatsu, kamar yadda majiyar ta bayyana.