Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na huɗu— bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 47,107 a yankin — sannan mahukuntan Tel Aviv sun ci gaba da kai farmaki a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Laraba, 22 ga Janairu, 2025
2100 GMT — Motocin agaji aƙalla 2,400 sun shiga Gaza
Kimanin motocin agaji 900 sun shiga Gaza a yayin da wani babban jami'i na MDD ya ce kawo yanzu babu wani ƙalubale da ya shafi karya doka.
Hakan na nufin a jumlace motocin agaji 2,400 sun shiga yankin wanda aka mamaye.
A watanni 15 da Isra'ila ta kwashe tana yaƙin kisa ƙare-dangi a Gaza, MDD ta bayyana shigar da kayan agaji yankin a matsayin babban ƙaluale — inda dakarun Isra'ila suke hana ma'aikatanta gudanar da ayyukansu sannan gungun 'yan Isra'ila suna sace kayan na agaji.
Muhannad Hadi, wani babban jami'i na MDD a Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ya ce a kwana uku da suka wuce ba a samu satar kayan agaji da yawa ba, "ba kamar a baya ba."
2000 GMT — An gano gawawwaki da suka zagwanye a ƙarƙarshin ɓuraguzan gidaje
Falasɗinawa da dama a birnin Rafah na kudancin Gaza sun koma gidajensu sai dai sun yi matuƙar kaɗuwa da ganin yadda aka wawashe komai a shaguna da gidajen nasu.
Manal Selim, wata mata mai 'ya'yan shida, da ke sana'ar gyaran gashi kuma tana da kantun sayar da kayan aure na mata, ta ce an sace komai daga shaguna da gidanta.
"Mun yi tsammanin za mu samu wani abu, ko kuma mu samun wurin zama," in ji ta. . "Ɓarnar ta girgiza mu."
A nasa ɓangaren, wani ma'aikacin agaji ya ce sun gano gawawaki da dama a ƙarƙashin ɓuraguzan gine-gine da Isra'ila ta ruguza.
"A cikin kwana biyu mun gano gawwaki 120 da suka zagwanye. Sun yi matuƙr zagwanyewa ta yadda ƙasusuwa ne kawai suka rage," a cewar Haitham Hams a hira da The Associated Press.