Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: 'Yan jarida 92 Isra'ila ta kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba

1420 GMT — 'Yan jarida 92 Isra'ila ta kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba

Akalla 'yan jarida 92 Isra'ila ta kashe a hare-haren da take kaiwa a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda ofishin watsa labarai na Falasdinu ya tabbatar.

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce 'yan jarida na baya-bayan nan da aka kashe sun hada da Rami Badir da Assem Kamal Musa wadanda aka kashe a lokacin da Isra'ila ta kai wani samame kwanaki biyu da suka gabata.

Ofishin bai yi karin bayani kan yadda aka kashe 'yan jaridar ba.

1155 GMT — Isra'ila ta kara kama Falasdinawa 20 a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun kama karin Falasdinawa 20 a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Lahadi a samamen da Isra'ilan ke ci gaba da kaiwa.

Zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da Isra'ilar ta kama a sun kai 4,4560 tun daga 7 ga watan Oktoba.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa wadda hukumar da ke kula da sha'anin fursunoni da tsaffin fursunoni da kuma kungiyar Fursunoni ta Falasdinu, akasarin wadanda aka kama an kama su ne a Hebron da Bethlehem da Ramallah da Nablus da Tulkarim da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai samame a Gabar Yamma da Kogin Jordan. / Hoto: Reuters

1056 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 47 a safiyar Lahadi, daga ciki har da 'yan gudun hijira

Falasdinawa akalla 47 aka bayar da rahoton cewa Isra’ila ta kashe a wasu hare-haren sama da aka kai a birnin Jabalia da sansanin ‘yan gudun hijira na Deir Al-Balah a Zirin Gaza, kamar yadda kafar watsa labaran Falasdinu ta ruwaito.

“Falasdinawa 35 aka kashe gommai kuma suka samu rauni a ranar Lahadi a lokacin da Isra’ila ta tayar da bam a wani gida da ke birnin Jabalia a arewacin Zirin Gaza,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ya ruwaito.

Wasu mazauna yankunan sun tabbatar da cewa akwai wasu mutum 90 wadanda aka raunata wasu kuma na karkashin baraguzai.

Isra'ila na ci gaba da kashe Falasdinawa akasari yara da mata a hare-haren sama da kasa. / Hoto: Reuters

"Jirigin yakin Isra'ila ya kuma kai hari wani gida da ke sansanin 'yan gudun hijira na Deir al-Balah wanda ke a tsakiyar Zirin Gaza, inda ya halaka akalla mutum 12 da raunata gommai, wadanda akasarinsu jama'ar da a baya suka rasa muhallansu ne," kamar yadda hukumar ta bayyana.

#