Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: WHO ta ce ta kasa tuntubar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa

0940 GMT — Sojojin Isra'ila sun kara kashe wani matashi a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun kara kashe wani Bafalasdine a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Lahadi, lamarin da ya ja adadin Falasdinawan da aka kashe a gabar ya kai 186, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta tabbatar.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce “Sojojin Isra’ila sun harbe Montaser Muhammad Amin Saif mai shekara 34 a ranar Lahadi a kauyen Burqa da ke arewacin Nablus.”

Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ce sojojin sun shiga kauyen na Burqa inda suka yi bincike a gidaje da dama.

0910 GMT — WHO ta ce ta kasa tuntubar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa

Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus a safiyar Lahadi ya tabbatar da cewa babu wata hanya da kungiyarsa ta WHO za ta tuntubi asibitin Al-Shifa da ke Zirin Gaza.

“WHO ta rasa hanyoyin sadarwa tsakaninta da cibiyarta da ke Asibitin Al-Shifa da ke Gaza, a daidai lokacin da ake samun rahotanni masu ban tsoro na karin hare-hare,” kamar yadda Tedros ya bayyana a shafin X.

Mista Tedros ya bayyana cewa wasu rahotanni sun ce wasu da suka gudu daga asibitin an harbe su inda aka kashe su, wasu kuma an ji musu rauni.

#