Tsawon kwanaki 109, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000.
1350 GMT — Tankokin yakin Isra'ila sun yi luguden wuta a Asibitin Nasser a Gaza
Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta kai tsaye a wani asibiti da ke kudancin birnin Khan Younis, inda fararen hula suka shiga cikin wani kazamin fada.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, tankokin Isra'ila na yin luguden wuta sosai a saman benayen sashe na musamman na aikin tiyata da kuma ginin gaggawa na Asibitin Nasser.
1222 GMT — An yi wa cibiyoyin lafiya ƙawanya a Khan Younis — Ma'aikatar Lafiya
Hukumomin Lafiya na Falasdinu sun ce sojojin Isra'ila sun kewaye wasu cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu a Khan Younis da ke kudancin Gaza.
A cikin wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Lafiya Ashraf al Qudra ya fitar, ya ce "Isra'ila ta sanya Cibiyar Lafiya ta Nasser da Asibitin Al Amal da ke Khan Younis cikin babban hadari."
Ya yi kira da a ba da kariya ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da marasa lafiya da ma’aikatan lafiya a cibiyoyin biyu tare da ba da damar kai musu daukin gaggawa.
1125 GMT — Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ƙara kutsawa Gaza bayan kashe mata sojoji 24
Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ci gaba da yaƙin da take yi a Gaza har sai "ta cimma nasara" duk da wahala mafi muni da ta fuskanta a ƴan kwanakin nan a yaƙin.
"Jiya mun sha matuƙar wahalar da ba mu taɓa sha ba tun da aka fara yaƙin nan," in ji Netanyahu.
"Ba za mu daina yaƙi ba har sai mun cimma nasara."
Ya ce rundunar soji na "bincike kan bala'in da ya faru" inda aka kashe sojojin ƙsar 21 a lokacin da bam ya fashe a wani gini a tsakiyar Gaza, lamarin da ya jawo Isra'ila ta rasa soja 24 a cikin kwana guda kacal.
1029 GMT — Ana ci gaba da ƙoƙrin sasantawa a kan batun Gaza, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar
Ana ci gaba da ƙoƙarin sasantawa don kawo ƙrshen yaƙin Isra'ila a Gaza, a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar a wani taron manema labarai.
Ya ƙara da cewa, ta'azzarar tashin hankalin da ake samu a Tekun Maliya alama ce ta "babban tashin hankali."
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da dakarun Birtaniya suka kai sabbin hare-haren sama a kan ƙungiyar Houthi da ake da alaƙa da Iran, waɗanda suke lalata harkokin kasuwancin jiragen ruwa don nuna adawarsu da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.
1117 GMT — Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-bauna
Sojojin Isra’ila a ranar Talata sun tabbatar da cewa akalla dakarunsu 21 Hamas ta kashe tare da raunata da dama a harin kwanton-ɓauna daya da aka kai musu a Zirin Gaza.
A wata sanarwa, mai magana da yawun sojojin kasar Rear Adm. Daniel Hagari ya ce lamarin ya faru ne kusa da iyakar Kissufim a daidai lokacin da Hamas din suka kai hari kan sojojin.
Ya bayyana cewa Hamas sun harba makamin roka kan wata tankar yaƙin Isra’ila inda kuma a lokacin wani tashin bam ya rusa wani gini mai hawa biyu.