Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 59 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falaadinawa fiye da 15,523, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 41,316 sun jikkata.
1345 GMT — Qatar za ta ci gaba da kokarin dawo da tattaunawar sulhu don tsagaita wuta a Gaza: Firaiminista
Qatar za ta ci gaba da kokarinta da sauran kasashen duniya na dawo da tattaunawar sulhu don tsagaita wuta a Gaza da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta
Firaiminista kuma Ministan Harkokin Waje Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani ya bayyana a cikin jawabinsa yayin taron Majalisar Ministoci karo na 158 na zaman taro na 44 na kasar Qatar ya ce: "Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta sanar da cewa, an gudanar da taron koli na kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf (GCC) a birnin Doha."
Al Thani ya sake nanata cewa "Qatar ta yi Allah wadai da laifuffukan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta aikata tare da yin kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa cikin gaggawa ba tare da nuna son kai ba kan wadannan laifuka, musamman hare-haren da aka kai kan fararen hula, da agaji da wuraren jinkai."
0130 GMT — Matasa da mata a Amurka suna adawa da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza
Galibin mata da matasa na Amurka ba su amince da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza ba, kamar yadda wani bincike da wata kungiya mai ra'ayin mazan jiya mai cibiya a Amurka, Gallup ta yi a kan mutum 1,013 ya nuna.
Sakamakon binciken da aka gudanar a watan jiya kuma aka fitar a wannan makon ya nuna cewa kashi 52 cikin 100 na mata da kashi 67 cikin 100 na matasa masu shekaru 18 zuwa 34 ba sa goyon bayan hare-haren Isra'ila.
Yayin da kashi 44 cikin 100 na mata ke goyon bayan hare-haren Isra'ila, wannan adadi ya karu zuwa kashi 59 na maza, yayin da kashi 37 cikin 1000 na matasa maza ke adawa da hare-haren.
Bakaken fata da Hispayawa da mutanen Asiya da na Tsibirin Pacific da ’Yan asalin ƙasar Amurka ba sa goyon bayan hare-haren da kashi 64 cikin ɗari, yayin da kashi 61 cikin 100 na fararen fata ke goyon bayan hakan.
A bangaren jam'iyyu kuwa, kashi 63 cikin 100 na 'yan Democrat ba su amince da harin da Isra'ila ke kai wa ba, inda kashi 36 cikin 100 ke goyon bayanta, yayin da kashi 71 cikin 100 na 'yan jam'iyyar Republican suka nuna amincewarsu, yayin da kashi 23 ne kawai suka ki amincewa.
0100 GMT — Sojojin Isra'ila za su yi 'yaki sosai' a kudancin Gaza
Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta za su yi yaki da mayakan Hamas a kudancin Gaza “kamar yadda suka yi a arewaci.”
"Mun yi yaki sosai kuma cikakke a arewacin Gaza kuma za mu yi hakan a kudanci,” in ji Shugaban Rundunar Sojin Isra'ila Herzi Halevi.
Halevi ya kai “ziyara ga Rundunar da ke Gaza inda ya tattauna da sojojin da ke can,” a cewar wata sanara da sojojin suka fitar.
A gefe guda, Gidan Rediyon Sojin Isra'ila ya bayar da rahoton cewa sojojin sun soma kai hari ta kasa a kudancin Gaza.
Ya ce sun soma kai hare-haren da daga arewacin Khan Yunis.
0030 GMT — Kungiyar Houthi a Yemen ta ce ta kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila 2 a Bahar Maliya
Kungiyar Houthi ta kasar Yemen ta ce ta kai hari da rokokin ruwa da jirgi mara matuki kan jiragen ruwan Isra'ila biyu a Zirin Bab al Mandab da ke Bahar Maliya.
“Dakarun Rundunar Sojojin Ruwa na Yemen sun kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila biyu a Zirin Bab Al Mandab, masu suna Unity Explorer da jirgi Number Nine, inda aka kai hari da rokokin ruwa kan jirgin ruwan farko sannan aka kai hari da jirgi mara matuki a kan jirgin ruwa na biyu,” a cewar kakakin rundunar Yahya Saree.
Saree ya ce “an kai harin ne bayan jiragen ruwan biyu sun ki sauraren gargadin da Rundunar Sojin Ruwan Yemen ta yi musu.”
“Rundunar Sojojin Yemen tana ci gaba da hana jiragen ruwan Isra'ila daga yin kara-kaina a Bahar Maliya da Kogunan Yankin Larabawa har sai Isra'ila ta daina kai hare-hare kan 'yan uwanmu da ke Gaza,” in ji shi.