Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 310, inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 39,790 — mafi yawansu mata da yara — ya kuma jikkata sama da mutum 91,702. Ana ƙiyasin fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa.
0610 GMT — Sojojin Isra'ila sun umarci mazauna Khan Younis su yi hijira daga unguwar Al Jalaa wanda a baya wuri ne da sojojin suka ayyana a matsayin "yanki mai aminci".
Unguwar Al-Jalaa ba za ta ci gaba da kasancewa a matsayin “wuri mai aminci ba,” in ji sanarwar sojojin.
Ta yi iƙirarin cewa mayaƙan Hamas na “aiki” daga unguwar tare da cewa wurin zai kasance “wuri mai hatsari na yaƙi.”
Duk da cewa a baya sojojin Isra’ila sun rinƙa ayyana wasu wuraren a matsayin “masu aminci,” amma suna ci gaba da kai munanan hare-hare a wuraren tare da jawo mutuwar Falasɗinawa da dama.