Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 82 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,915, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,918.
0703 GMT — Sojojin Isra'ila sun ce an kashe karin dakarunsu a yakin arewacin Gaza
Sojojin Isra'ila sun sanar da kashe wasu dakarunsu uku a arangamar da suka yi da mayakan Falasdinawa a arewacin Gaza yayin da Isra'ila ke kara kai hare-hare a cikin Gaza, inda tuni aka ce an kashe kusan mutum 21,000.
A cikin wata sanarwa da jaridar intanet ta Times of Israel ta buga, sojojin Isra'ila sun bayyana cewa sojojin uku su ne da Laftanar Yaron Eliezer Chitiz, mai shekara 23 da mataimakin kwamandan rundunar Givati Brigade, Staff Sgt. Ita Buton mai shekara 20, da kuma Staff Sgt. Efraim Jack man mai shekara 21, dukansu daga rundunar Givati Brigade.
A cikin wata sanarwa da ta fitar tun da fari, sojojin Isra'ila sun kuma sanar da kashe sojoji biyar da suka hada da kwamandoji a Gaza, baya ga jikkata sojoji 43 da tara daga cikinsu na cikin mawuyacin hali a Gaza.
Zuwa yanzu an kashe sojojin Isra'ila 164 a Zirin Gaza tun bayan fara mamayar da ƙasar ta yi a yankin da ta yi wa ƙawanya a ranar 27 ga watan Oktoba.
0500 GMT — Za a kwashe 'karin watanni da dama' ana luguden wuta a Gaza — Shugaban Rundunar Sojin Israila
Shugaban rundunar sojin Isra'ila ya yi gargadin cewa za su kwashe "karin watanni da dama" masu zuwa suna yin luguden wuta a Gaza, inda kawo yanzu aka kashe Falasdinawa kusan 21,000.
Shugabannin Isra'ila sun sha alwashin matsa kaimi wurin kai hare-hare har sai sun kawar da kungiyar Hamas da ke fafutukar kare hakkin Falasdinawa, kuma shugaban rundunar sojin Herzi Halevi ya nuna alamawar cewa babu wata hanya ta kawo karshen yakin cikin gaggawa.
"Babban burin wannan yaki yana da muhimmanci kuma cim masa ba abu ne mai sauki ba," in ji Halevi ranar Talata da maraice.
0126 GMT — Amurka da Isra'ila sun tattauna yakin Gaza
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro a Fadar White House Jake Sullivan, da Ministan kula da tsare-tsare na Isra'ila, Ron Dermer, sun tattauna kan shirin da za a yi a wannan rana, bayan mummunan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya, ciki har da harkokin mulki da tsaro, in ji wani jami'in Fadar White House.
Sullivan da Dermer sun kuma tattauna kan kokarin dawo da sauran fursunonin gida da kuma sauya sheka zuwa wani mataki na daban na yakin don kara mayar da hankali kan manyan manufofin Hamas, a lokacin da suka hadu, in ji jami'in.
Sojojin Isra'ila sun fadada farmakin da suke yi a sansanonin 'yan gudun hijira na birane a tsakiyar Gaza bayan da suka yi ruwan bama-bamai kan al'ummar Falasɗinu mai cunkoso tare da umurtar mazauna yankin da su gudu.
Duk da kiraye-kirayen da Amurka ta yi ga Isra’ila da ta dakatar da asarar fararen hula da kuma matsin lamba daga kasashen duniya na tsagaita wuta, Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce sojojin na kara zurfafa kai hare-hare.
0029 GMT — Kasar Cuba ta caccaki 'ƴar ta'adda' Isra'ila
Shugaban kasar Cuba ya yi kira da a kawo karshen mummunan yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, wanda aka shafe fiye da watanni biyu da rabi ana gwabzawa.
"Kisan kiyashin da 'yan ta'adda Isra'ila ta aikata a Gaza abin kunya ne ga dukkan bil'adama, har yaushe za a yi hukunci a kai? Har yaushe za a sami 'yancin yin kisan kai? Cuba, wadda ba za ta taba kasancewa cikin masu halin ko-in-kula ba, tana ɗaga murya don kare Falasɗinu, akai-akai, ”in ji Miguel Diaz-Canel a shafinsa na X.
Kasar da ke kan tsibiri dai ta sha yin Allah wadai da tashe-tashen hankulan da ake yi a Falasdinu, har ma majalisar dokokin Cuba ta bayyana goyon bayanta ga al'ummar Falasdinun.
A ranar 20 ga watan Disamba, majalisar dokokin Cuba ta yi Allah wadai da "kashe dubban Falasdinawa a Zirin Gaza, fiye da kashi 70% na yara da mata, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ta kai tun ranar 7 ga watan Oktoba."
Sanarwar ta ce "Halin da ake ciki a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon shekaru 75 da Isra'ila ta yi na mulkin mallaka da mamaya ba bisa ƙa'ida ba, tare da take hakkin al'ummar Falasdinu a yankunansu."
2053 GMT — Houthi sun kai hari kan jirgin ruwa a Tekun Maliya; Amurka ta harbo jirginsu marar matuki
'Yan tawayen Houthi na Yaman sun yi ikirarin kai hari da makami mai linzami kan wani jirgin ruwa a Bahar Maliya da kuma wani hari da wani jirgi mara matuki ya kai wa Isra'ila tare da hadin gwiwar Falasdinawa da ke Gaza.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, 'yan tawayen sun ce "sun kai farmaki kan wani jirgin ruwa na kasuwanci" da suka kira da MSC UNITED, tare da harba jiragen sama masu saukar ungulu a kudancin Isra'ila.
Amurka bayan kai harin, ta yi ikirarin cewa dakarunta sun harbo jiragen sama marasa matuka da wasu makamai masu linzami da 'yan tawayen Houthi suka harba.
"Babu rahoton lalata jiragen ruwan ko jikkata wasu da ke ciki," in ji babban kwamandan tsaron na Pentagon a wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta, inda ya bayyana cewa an kai harin da jiragen sama marasa matuka guda 12, da makamai masu linzami guda uku cikin tsawon awa 10.