Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 143 - ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa aƙalla 29,692, galibi yara da mata, tare da jikkata wasu 69,879.
0100 GMT — Sojin Isra'ila sun gabatar da shirin kwashe mutane yayin da Netanyahu ya sha alwashin mamaye Rafah
Sojojin Isra'ila sun gabatar da wani shiri na "kwashe" fararen hula daga Gaza, bayan da Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce kai farmaki ta ƙasa kan birnin Rafah na kudancin Falasdinawa ya zama wajibi domin samun nasara baki ɗaya.
Gwamnatocin ƙasashen waje da ƙungiyoyin agaji sun sha bayyana fargabar cewa irin wannan farmakin zai janyo asarar rayukan fararen hula a Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.4 -- galibinsu da suka yi gudun hijira daga wasu yankuna -- suke samun mafaka a can.
Har ila yau, ita ce hanyar shigar da agajin da ake tsananin buƙata, inda ake shigar da kayayyakin daga maƙwabciyarta Masar.
Sojojin Isra'ila "sun gabatar wa da majalisar ministocin yaƙin wani shiri na kwashe jama'a daga yankunan da ake gwabzawa a Gaza, da kuma shirin gudanar da aikin ƙaddamar da hare-hare da ke tafe", a wata sanarwa da ta fito daga ofishin Netayahu a cikin harshen Hebrew a yau Litinin.
Sanarwar ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda za a kwashe fararen hular ko kuma inda za a kai su ba.
Sanarwar ta zo ne bayan da ƙwararru da Masar, Qatar da Amurka suka gana a birnin Doha, taron da ya kuma samu halartar wakilan Isra’ila da na Hamas, kamar yadda kafar yada labarai ta Masar mai alaƙa da gwamnatin Masar ta bayyana, wanda shi ne yunƙuri na baya-bayan nan da aka yi na ganin an cimma matsaya kafin watan Ramadan mai alfarma.
2311 GMT — Isra'ila ta sha alwashin kai hari kan ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon ko da kuwa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a Gaza
Ministan tsaron Isra'ila ya sha alwashin zafafa kai hare-hare kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Lebanon ko da an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a Gaza.
Kungiyar Hizbullah da ke musayar wuta da Isra'ila a tsawon yaƙin da take yi a Gaza, ta ce za ta dakatar da kai hare-hare kusan kullum a kan Isra'ila idan har aka tsagaita wuta a Gaza.
Amma Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce duk wanda ya yi tunanin tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza na nufin zai yi amfani a yankin arewacin ƙasar to "bai fahimci abin ba."
"Za mu ci gaba da ɓarin wutar da muke yi," in ji Gallant. Ya ce, akwai wata manufa mai sauƙi, ita ce ta kawar da Hizbullah daga kan iyakar Isra'ila, ko dai ta hanyar yarjejeniyar diflomasiyya ko kuma da ƙarfi.