Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0332 GMT — Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila a Gaza
Shugaban Hamas Isma'il Haniyeh ya ce ƙungiyar gwagwarmayarsa na gab da cimma yarjejeniyar sulhu da Isra'ila, a cewar wata sanarwa da aka wallafa ta kafar Telegram.
"Ana gab da cimma yarjejeniya kan sulhu," in ji Haniyeh, a cewar sanarwar
Masu shiga tsakani sun yi ta ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya don ba da damar sakin kusan fursunoni 240 da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, a lokacin harin da aka kai wa Isra'ila mafi muni a tarihinta.
Mayakan Hamas sun kuma kashe mutum kusan 1,200 a harin da suka kai kan iyaka.
Isra'ila ta kaddamar da hare-haren bama-bamai ba tare da bata lokaci ba tare da kai farmaki ta kasa a matsayin ramuwar gayya kan harin, inda ta lashi takobin rusa Hamas tare da ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
0117 GMT — Jami'in WHO ya ce halin da asibitin Gaza ke ciki ya zama 'bala'i'
Wani babban jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya bayyana halin da ake ciki a asibiti a Gaza a matsayin "mummunan bala'i", yana mai cewa yawanci ba sa aiki kuma abin da ya rage zai iya durkushewa sakamakon dubban haihuwar da ake sa ran mata za su yi a wata mai zuwa.
Bayanin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne sa'o'i kadan bayan da wani hari da aka kai ya shafi hawa na biyu na wani asibiti a arewacin Gaza, inda ya kashe mutum 12, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da kuma wani ma'aikacin lafiya.