Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ya shiga kwanaki 294, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,175 - akasarinsu mata da yara - tare da jikkata mutum 90,403, kana an ƙiyasta cewa an binne fiye da mutum 10,000 a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.
Juma'a, 26 Yuli, 2024
2300 GMT — Wani shugaban Falasɗinawa da ke da alaƙa da Hamas a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya mutu a hannun Isra’ila sakamakon tsananin rashin lafiya, a cewar wata ƙungiyar gwamnati ta Falasɗinu.
Mustafa Muhammad Abu Ara, mai shekaru 63, ya rasu ne bayan da aka kai shi asibiti daga gidan yarin Ramon da ke kudancin Isra'ila, in ji wata sanarwa da hukumar kula da fursunonin Falasɗinu ta fitar.
"Kafin a kama shi, yana fama da rashin lafiya mai tsanani da ke buƙatar kulawa sosai, amma tun daga lokacin da aka kama shi, Sheikh Abu Ara, kamar sauran fursunoni, yake fuskantar wulaƙancin da ba a taɓa ganin irinsa ba tun farkon yaƙin.''
2222 GMT — Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasɗinawa 6 da Isra'ila ta yi a gidajen yarinta
Ƙungiyar Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasɗinawa shida waɗanda suka haɗa da mata biyu da aka sako daga gidajen yarin Isra'ila.
A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta bayar da misali da shaidar da ta samu daga wurin fursunonin da aka sako wadda kamfanin dillancin Labarai na Anadolu ya tattaro.
Falasɗinawa sun bayyana cewa sun fuskanci "mummunar azabtarwa da duka a tsawon lokacin da suke tsare."
Hamas ta ce azabtarwar da aka yi musu "tana nuna yanayin da dubban fursunoni da sauran Falasɗinawan da aka tsare suke fuskanta a mamayar Isra'ila da kuma hukunci a cibiyoyin tsarewa irin salon 'yan Nazi."
Kazalika ƙungiyar ta jaddada cewa irin wannan azabtarwa, ''waɗanda ba su da imani da tausayi da sanin ƙima da darajar ɗan'adam ne suke aiwatar wa a kan mutane masu rauni da ba su ji ba ba su gani ba.''
Ta ce fursunonin da aka sako "sun nuna alamun rashin lafiya saboda azaba da sakaci da yunwa da zagi da kuma rashin barci da suka fuskanta," tana mai ƙira kan a gaggauta daukar mataki mai tsauri don fallasa abubuwan da ke faruwa a gidajen yarin Isra'ila da kuma ceto dubban Falasdinawa da ake tsare da su a wannan wuri- da ake aiwatar da salon tsarewa irin na Nazi.''
0036 GMT — Falasɗinawa da Yahudawa sun gudanar da zanga-zangar lumana
Ɗaruruwan Falasɗinawa da Yahudawa na Isra'ila ne suka yi ta rera taken "E, a samu zaman lafiya, e, ga yarjejeniya", a yayin wani tattaki da suka yi a birnin Tel Aviv, suna masu neman a kawo ƙarshen kashe-kashe da ake yi a Gaza.
Masu zanga-zangar sun ce ajandarsu ta farko ita ce a tsagaita wuta a yankin da aka mamaye, amma gaba ɗaya suna so a sake maido da dangantakar Falasɗinu da Isra'ila tare da ba da damar kafa sabuwar rayuwa.
2044 GMT — Masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu sun yi zaman dirshan a kusa da Fadar White House
Masu zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya, sun gudanar da 'zaman dirshan' a tsallaken wurin shaƙatawa na Lafayette da kuma Fadar White House a yayin ganawar Shugaba Joe Biden da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Masu zanga-zangar sun zuba jan ruwa a kan titi, suna masu cewa hakan na nuni da jinin waɗanda aka kashe a Gaza.
Kazalika sun yi ta rera taken "A kama Netanyahu" tare da nuna hoton Firaministan sanye da wata riga mai launin ruwan lemu da ke da jini, kana an yi rubutu a kai da ke cewa "A kama shi da laifin take hakkin ɗan'adam."