Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 33 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,297, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000.
Alhamis, 10 ga Fabrairun 2025
2135 GMT — Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sake jaddada cewa kasarsa ba ta sayarwa ba ce, kuma ya yi watsi da duk wani kira na a kori al'ummar Falasdinu.
Hakan ya zo ne a lokacin bude taron kwamitin kolin Fatah a Ramallah da ke tsakiyar Gabar Yammacin Kogin Jordan, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu, WAFA.
Yayin da yake misali da halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka a Addis Ababa da ya yi, wanda aka kammala ranar Asabar, Abbas ya bayyana cewa, ya jaddada matsayar Falasdinu kan duk wani yunƙuri na raba al'ummar Falasdinawa.
"Falasdinu ba ta sayarwa ba ce," in ji shi, yana mai nanata "tabbatacciyar matsayar Falasdinawa cewa ba wani yanki nata - ciki har da Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, ko Kudus - da za a yi ƙwace."
Ƙarin labarai ????
2345 GMT — Isra'ila ta ci gaba da yin watsi da alkawurran da ta dauka na tsagaita wuta: Sojojin Lebanon
Sojojin kasar Labanon sun zargi Isra'ila da ci gaba da kauce wa alkawurran da ta dauka karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma keta hurumin kasar Lebanon.
A martaninta na farko a hukumance game da mamayar da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankunan kan iyaka guda biyar a kudancin Lebanon, sojojin sun tabbatar da cewa dakarunta na ci gaba da aikewa da su zuwa dukkan garuruwan da ke kan iyaka da ke kudancin kasar tare da hadin gwiwar kwamitin Quintet da ke sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta da dakarun MDD a Lebanon (UNIFIL) bayan janyewar sojojin Isra'ila daga wadannan yankuna.
Rundunar sojin Isra'ila ta ci gaba da zama a wurare da dama na kan iyaka da ke cikin kasar Lebanon, suna ci gaba da kauce wa alkawuran da suka dauka tare da keta hurumin kasar Labanon ta hanyar ci gaba da cin zarafi ga tsaron kasar Lebanon da 'yan kasar.