Yakin da Isra'ila ke yi a kan Falasdinawa da ke Gaza - wanda ke cikin kwanaki na 157 - ya kashe akalla mutane 31,045, galibi yara da mata, tare da raunata 72,654.

Kai-tsaye: Sarkin Saudiyya ya yi kira kan kawo ƙarshen 'munanan laifukan' da ake yi a Gaza

0140 GMT — Sarkin Saudiyya ya yi kira kan kawo ƙarshen 'munanan laifukan' da ake yi a Gaza

Sarki Salman na Saudiyya ya yi kira a cikin saƙonsa na watan Ramadan ga ƙasashen duniya da su kawo ƙarshen munanan laifukan da ke faruwa a Gaza, inda Isra'ila ta shafe sama da watanni biyar tana gwabza yaƙi a yankin.

Da yake magana a matsayin mai kula da wurare biyu mafi tsarki na Musulunci, Sarki Salman ya yi godiya kan “yadda aka albarkaci Masarautar Saudiyya”, amma ya ce yaƙin da ake yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya zai sa a yi azumi da sauran ibadu cikin rashin walwala.

“Yayin da muke maraba da shigowar watan Ramadan a wannan shekara, zukatanmu sun yi matukar bacin rai kan yadda ‘yan'uwanmu Falasɗinawa ke ci gaba da fuskantar hare-haren wuce gona da iri,” in ji shi.

"Muna kira ga ƙasashen duniya da su kiyaye nauyin da ke wuyansu na kawo ƙarshen waɗannan munanan laifuka tare da tabbatar da kafa hanyoyin jinƙai da na agaji."

2300 GMT —

Sojojin Isra'ila sun gano an harba rokoki 30 daga Lebanon zuwa Tuddan Golan

Gidan rediyon rundunar sojin Isra'ila ya bayyana cewa, an harba rokoki 30 daga ƙasar Lebanon zuwa garin Majdal Shams da ke yankin Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye, wanda ya zo daidai da ƙarar jiniya.

Gidan rediyon bai fayyace ko an samu asarar rayuka ba.

Ba a bayar da rahoton ko wasu sun ɗauki alhakin kai harin ba.

A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce ta gano mayaƙa ɗauke da makamai masu linzami a yankin gonakin Shebaa da ke kudancin kasar Labanon kuma jiragenta biyu sun kai musu hari kafin su harba makaman.

2100 GMT — Jirgin ruwan Red Crescent na Turkiyya ya isa Masar ɗauke da kayan agaji ga Gaza

Jirgin ruwan Bayar da Agajin Gaggawa na Turkiyya na Bakwai dauke da kayan agaji ga Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya ya isa tashar ruwan El Arish ta Masar.

Kayayyakin agajin da ake bukata za su shiga Gaza ta Masar, a kan iyakar Rafah da ke kudancin kasar.

Jirgin yana ɗauke da kaya sama da ton 2,700 da suka hada da buhunan abinci da ke dauke da shiryayyen abinci da ruwa da fulawa da tufafi da kayan tsafta da kayan matsuguni kamar tanti da jakunkuna da barguna da kayan aikin likita da kayan jarirai.

#